Gwamnatin Tarayya ta bayyana ‘yan adawar da ke sukar Shugaba Muhammadu Buhari cewa ba su da kunya, kuma a adawa za su ƙare.
Ministan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
PDP da LP dai sun maida wa Buhari Kakkausan raddi, bayan ya bayyana dalilan da ya ce su ka haifar da faɗuwar masu adawa zaɓen 2023.
PREMIUM TIMES Hausa ta ruwaito Buhari ya bayyana abin da ya ce ya kayar da ‘yan adawa zaɓen shugaban ƙasa.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa jam’iyyun adawa sun faɗi zaɓen 2023 ne saboda ci-da-zuci da hangen-Dala, ba shiga birni ba.
Buhari ya ce wannan ci da zucin jam’iyyu ya bai wa APC ƙarfin samun sake yin nasarar kafa mulki ko kuma nasarar zaɓen 2023.
Buhari ya yi wannan fashin baƙin ne a lokacin da ya karɓi ziyarar Gwamnonin APC, bisa jagorancin Gwamna Atiku Bagudu wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC.
“Jam”iyyun adawa sun ɓata lokaci su na ta kiran masu goya masu baya daga ƙasashen waje cewa za su kayar da APC. Amma sai jam’iyyar mu ta yi masu kwasar-karan-mahaukaciya, ta zubar da su ƙasa.
“To yanzu ci-da-zucin su ya kai su ya baro su, maimakon nasara, sai matsalolin su ke ta ƙaruwa. Sun kasa bayyana wa masu goyon bayan su daga waje, gamsassun dalilan da ya sa su ka kasa kayar da mu zaɓe.”
Buhari ya shawarci gwamnonin APC su ƙara haɗa kai domin magance dukkan ƙalubalen da ke gaban su.
Buhari ya yi dogon bayani dangane da rayuwar sa bayan ya yi ritaya, ya ce zai shafe watanni shida a Daura, daga nan ya koma Kaduna baki ɗaya.
Buhari ya gode wa Gwamna Nasiru El-Rufai saboda ayyukan raya jihar da ya samar a Kaduna.
Ya ce gyaran da Buhari ya yi wa Kaduna zai sauƙaƙa masa yin rayuwa a cikin sauƙi idan ya tare a Kaduna, bayan ya yi watanni shida a Daura.
Bagudu ya ce sun je ne domin su yi wa Buhari Barka da Sallah kuma su yi masa fatan alheri.
Da ya ke wannan ce siyasar su ta farko tun bayan kammala zaɓe, gwamnonin sun taya Buhari murnar sake lashe zaɓe da APC ta yi.
A cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Lai, Segun Adeyemi ya fitar a ranar Lahadi, Ministan Yaɗa Labarai ya ƙara nanata duk abin da Buhari ya faɗa a kan jam’iyyun siyasa.
Ya ce dukkan su sun fi maida hankali wajen ganin sun yaudari masu goya masu baya daga ƙasashen waje, waɗanda su ka tabbatar wa cewa su ne za su yi nasara, ba APC ba.
“Kowa ya san APC ta ci zaɓe na gaskiya, babu maguɗi. Idan aka duba, APC ba ta yi nasara a jihar Shugaba Buhari ba, a lokacin zaɓen shugaban ƙasa. To shi kuma Buhari da ya tsoma baki a zaɓe a yi ba daidai ba, ya gwammace APC ta faɗi a jihar ta sa.” Cewar Lai.
Ya ce dukkan ‘yan takarar da ke ta kartar ƙasa da karakainar zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe, babu wanda ya samu sakamakon da za’a ce har ya na da bakin yin ƙorafi ko ƙwarin-guiwar zuwa kotu.
Discussion about this post