Ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC na Jihar Ribas, Tonye Cole, ya bayyana yadda ‘yan ta-kifen PDP su ka kikkifa masa mari a ofoshin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
Cole ya ce ba marin kaɗai ya sha ba, an kuma riƙa jifar sa da ruwan ‘pure water’, sannan aka riƙa labta masa abinci a jiki.
Ya ce ya je ofishin INEC ne domin hukumar ta ba shi kwafe-kwafe na takardun bayanan da ya ke buƙata domin ya kafa hujja da su a ƙarar da ya shigar, wadda ya ke jayayya da nasarar da INEC ta ce ɗan takarar PDP na gwamnan Ribas ya yi.
Fubara na PDP ya samu 302,614, shi kuma Cole na APC ya samu 95,274.
Cole ya ce bai yarda da sakamakon zaɓen ba, ya ce zai je kotu a yi shari’a, tunda a cewar sa a tafka maguɗi.
Ya shaida wa Gidan Talbijin na Channels cewa tsageran PDP su ka hana shi da tawagar sa shiga ofishin INEC a ranar Litinin.
A ranar Juma’a shi da wasu shugabannin APC na Jihar Ribas sun kasa shiga ofishin tun a ranar Juma’a, amma su ka sha alwashin komawa a ranar Litinin ɗin nan.
Da ya ke bayyana irin yadda aka faffalla masa mafi, Cole ya ce gaskiya dimokraɗiyya akwai matsala a yanzu. “Ya kamata a ce INEC ta tanadi duk wasu kwafen takardun bayanan da ta san mai jayayyazai je ya nema. Saboda akwai takardun da idan mu ka kai su kotu, daga nan za mu gina hujjojin da za mu ci gaba da bayarwa.”
Ya ce sun je a ranar Juma’a, amma ko takardar tsire INEC ba ta ba su ba.
“Yau Litinin kuma mun je amma tsagerun PDP da ‘yan jagaliyar su sun hana mu shiga, su ka yi mana wulaƙanci, har da mari na da watsa min ruwa da abinci a jiki na.”
“Nan dai sai kawai mu ka fara jin ana harbe-harben bindiga. Da kyar jami’an tsaro na su ka fitar da ni a cikin rintsi, bayan an ji min ciwo, an dalla min mari. Har da duwatsu sun jefe ni.”
Cole ya ce ya gudu zuwa cikin ofishin INEC, amma aka bi shi har cikin ofis ɗin.
Discussion about this post