Shugabannin APC na Mazaɓar Kashere da ke cikin Ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe, sun baɗa wa idanun su toka, inda su ka take umarnin kotu, su ka bayyana korar Sanata Ɗanjuma Goje daga APC.
Sun kore shi ne bayan sun zarge shi da yi wa jam’iyya zagon ƙasa.
Shugabannin mazaɓar sun yi fatali da umarni da kotu ta bayar, wanda ta hana a bincike shi ko a ɗauki duk wani matakin ladabtarwa kan sa wato sanata Danjuma Goje.
An bayyana dakatar da tsohon Gwamnan Gombe kuma sanata a halin yanzu, a lokacin da Shugabannin APC na Mazaɓar Kashere su ka kira taron manema labarai, inda Shugaban Mazaɓar Tanimu Abdullahi ya ce sun yanke shawarar afka hukunci dakatarwa kan Goje, bayan da kwamitin bincike ya tabbatar da lallai ya yi wa APC zagon ƙasa.
Kafin a zo wannan gaɓar dai sai da Goje ya garzaya kotu, ya nemi a hana shugabannin mazaɓar sa kafa kwamitin binciken zargin da su ke masa, kuma a hana su tsige shi.
Dalilan Korar Goje Daga APC – Abdullahi, Shugaban APC, reshen ƙauyen su Goje:
Abdullahi ya ce daga cikin dalilai, akwai saboda Goje ya ƙaurace wa kamfen ɗin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Gombe. Sannan kuma ya ƙaurace wa kamfen din ƙauyen su, Shiyyar sa, da jiha baki ɗaya.
“Haka kuma an same shi da laifin goyon bayan wasu jam’iyyu masu adawa.