Babban kotu a jihar Jigawa ta yanke wa wasu mutane uku da suka shahara wajen yin garkuwa da mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta kuma yanke wa wani mai suna Mustapha Isah hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekara 10 bayan an same shi da laifin saduwa da maza ta dubura.
Alkali Mohammed Kaugama ya yanke wa Suleiman Bello, Auwalu Muhammed da Yakubu Muhammed hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan kotun ta kama su da laifuka 9 da suka hada da hada baki a cuci wani, kisa da fashi da makami.
Kaugama ya ce kotun ta gurfanar da wadannan mutane bisa laifin hada baki domin kashe wani Audi Saje mazaunin kauyen Manda dake karamar hukumar Kaugama. Mutanen sun sace babur din mutumin bayan da suka kashe shi.
Ya ce kotun ta kuma gano cewa mutanen yayin da suke fashi da makami sun yi garkuwa da Hadiza Abdullahi mazauniyar kauyen Marma dake karamar hukumar Kirikasamma sannan har sun bukaci a biya su Naira miliyan 150 kudin fansa.
Bayan haka kakakin ma’aikatar shari’a ta jihar Jigawa Zainab Baba ta ce jami’an tsaro sun kama wadannan mutane a maboyar su da makamai da suka hada da bindigogi kirar AK-47 guda uku, bindiga kirar GPMG daya, kudi Naira miliyan 2.7 da babur kirar ‘Boxer’ guda daya na marigayi Saje.
Daga nan wani alkalin kotu Mohammed Sambo ya daure Mustapha Isah mazaunin kwatas din Auramo dake karamar hukumar Ringim na tsawon shekara 10 bayan an kama shi da laifin yi wa maza fyade.
Ma’aikatar shari’a ta bayyana a kotun cewa Isah ya shiga shagon sa da wani yaro mai shekaru 11 yayi lalata da shi.
Da ya shiga hannun jami’an tsaro Isah ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi.
Discussion about this post