Kotun Grade 1 dake garin Ibadan, jihar Oyo, ta warware auren shekara 13 tsakanin Susan Udeze da mijinta Frank bisa zargin kisa.
Alkalin kotun S.M. Akintayo ta ce ta raba auren domin a samu zaman lafiya, kada a aikata dana sani.
Akintayo ta bai wa Susan ikon kula da ‘ya’yan su biyu da suka haifa tare sannan shi Frank zai rika biyan Naira 15,000 kudin ciyar da yaran.
Ta ce ma’auratan za su hada hannu domin ‘ya’yan su sun samu ilimin boko da biyan sauran bukatun su.
Akintayo ta ce daga yanzu Frank ba shi da ikon shiga rayuwar Susan sannan yana da ‘yancin ganin ‘ya’yan sa a duk lokacin da yake so.
Susan ta fara kai karan Frank a kotu a watan Janairu 2022 inda ta roki kotu ta raba auren ta kafin mijinta ya kashe ta.
Ta ce a kullum tana fargabar idan ta ci gaba da zaman aure da Frank wata rana zai yi ajalinta.
“Frank ya ce maiya ce sannan yakan kora ni daga cikin gidan mu baya lakada mun dukan tsiya da dare.
“Sau da yawa Frank na yi mun barazanar zai kwarara mun ruwan batir a fuska. Sannan ko da mahaifiyata ta rasu Frank ya nuna halin ko in kula.
Ko da yake kotun ta aika wa Frank sammace amma bai zo kotun ba.