Kotun majistare dake Okitipupa a jihar Ondo saurari shari’ar wani birkila mai suna Segun Bashiri mai shekaru 34 da ake zargin sa da sace buhunan simintin Dangote 50 da kudinsa ya kai naira 235,000.
Kotun ta gurfanar da Bashiri bisa laifuka da suka hada da hadin baki da sata.
Dan sandan da ya shigar da kara ASP Zedekiah Orogbemi ya ce Bashiri ya sace buhunan simintin ranar 12 ga Janairu da misalin karfe 12:30 na safe a wurin da yake aiki birkila a Oktipuoa-Ikoya dake Okitipupa.
Orogbemi ya ce Bashiri tare da wani abokinsa da suke aiki tare a wurin ginin wani Mathew Kawonise ne suka sace simintin.
Ya ce zuwa yanzu rundunar na ci gaba farautan abokin Bashiri da suka tafka wannan abu.
Bashiri dai a kotun ya musanta aikata abinda ake tuhumarsa da shi.
Alkalin kotun Chris Ojuola ya Bada belin Bashiri akan naira 100,000 tare da gabatar da shaidu biyu.
Ojuola ya ce Bashiri ya tabbatar cewa shaidun biyu din da zai gabatar na zaune ne wurin da kotun take da iko sannan su gabatar da shaidar sun biyan gwamnatin jihar Ondo haraji na tsawon shekara 2.
Za a ci gaba da shari’a ranar 6 ga Mayu.
Discussion about this post