Kotun dake sauraren kararrakin cin zarafin mata da yara kanana dake Ikeja jihar Legas ta gurfanar da babban faston cocin ‘ I Reign Christian Ministry’ Daniel Oluwafeyiropo bisa zargin yin lalata da wa wasu membobin mata biyu.
Alkalin kotun Ramon Oshodi ya yanke hukuncin daure Oluwafeyiropo a kurkukun Kirikiri har sai faston ya kammala cika sharuddan belin da ya bada.
Oshodi ya bada belin faston akan naira miliyan 20 tare da gabatar da shaidu biyu dake biyan haraji a jihar kuma suke zama a inda kotun take da iko.
Alkalin ya kuma ce faston ya tabbatar cewa daya daga cikin shaidun da zai gabatar ya mallakin gini ko fili dake da darajar kudin belin da kotun ta bada.
“Shaidan dake da mallakan fili ko ginin zai mika takardun filin ko ginin ga kotu.
“Shima faston zai mika da takardun tafiyarsa ga magatakardar kotun.
Za a ci gaba da shari’a ranar 9 ga Mayu.
Lauyan dake kare faston Olukunle Oyewole ya roki kotun ta bada belin faston sannan ya tabbatar cewa faston zai cika duka sharuddan belin da kotun da kmaka gindaya masa
Sai dai lauyan da ya shigar da karan Babjide Boye ya ki amincewa da belin da Oyewole ya nema yana mai cewa idan har aka saki faston zai iya amfani da matsayinsa wajen hana fannin da suka shigar da kara samun hujjoji masu kwari a kansa.
Duk da cewa faston ya musanta laifin da ake tuhumarsa akai bincike ya nuna cewa faston ya yi lalata da wadannan mata tun a watan Yunin 2020 a Ikota Villa ELekki dake Lekki.