Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta bayyana cewa ɗan takarar gwamnan Kebbi ƙarƙashin APC, Nasiru Idris ne ya yi nasarar lashe zaɓe.
Idris wanda a yanzu shi ne zaɓaɓɓen gwamnan Jihar Kebbi, ya lashe zaɓen ne bayan kammalawar da aka yi a ranar Asabar, 15 ga Afrilu, 2023.
INEC dai ta bayyana zaɓen Kebbi, Sokoto da Adamawa cewa ba su kammalu ba a ranar 18 Ga Maris.
An sake zaɓe a rumfunan zaɓe 142 a cikin ƙananan hukumomi 20 daga 21 na faɗin jihar.
Bayan kammala tattara sakamakon zabe ne sai Baturen Zaɓe Farfesa Yusuf Sa’idu daga Jami’ar Sokoto ya bayyana sakamakon cewa Idris na APC ya samu 409,225, shi kuma Aminu Bande na PDP ya tashi da 360,940.
Udu Idris na PRP ne mai ƙuri’u 3,103 ya zo na uku.
Baturen Zaɓe ya ce an jefa ƙuri’a har 800,560, waɗanda daga ciki 781,478 ne halastattu. Sauran 19,082 kuwa lalatattu ne, don haka INEC ta watsar da su.
Sokoto: Tambuwal Da Wammako Sun Zama Sanatoci:
A Jihar Sokoto kuwa, an bayyana cewa Gwamna mai barin gado, Aminu Tambuwal na PDP ya samu nasarar lashe zaɓen Sanatan Sokoto ta Kudu.
Tambuwal ya samu ƙuri’u 100,860, inda ya kayar da Ibrahim Ɗanbaba, wanda shi kai na APC mai ƙuri’a 95,884.
Shi kuma tsohon Gwamnan Sokoto kuma Sanata, Aliyu Wamakko na APC, wanda ke wakiltar Sokoto ta Arewa, ya lashe kujerar da ƙuri’u 141,448, inda ya kayar da Muhammadu Ɗan’Iya na PDP mai ƙuri’u 118,445.