Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya ce zargin da Atiku Abubakar ya yi masa na “harƙalla” a lokacin zaɓen shugaban ƙasa ba shi da hurumi a shari’a ko kaɗan.
Tinubu ya bayyana wa kotu wannan jayayya da ya ke yi da Atiku, inda ya ƙara da cewa babu inda a cikin ƙorafin da Atiku ya shigar a kotu ko a a wuri ɗaya, inda ya yi bayanin wurare ko wurin da ya ce an yi harƙallar.
Atiku wanda ya zo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa, shi da jam’iyyar sa PDP sun garzaya kotu, su na roƙon a soke zaɓen ko kuma a bai wa Atiku nasara, bisa ga zargin ɗibga maguɗi da su ka ce an yi a zaɓen na ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Atiku da PDP sun maka Tinubu, APC da INEC ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe.
APC da Tinubu sun maida wa Atiku da PDP raddin cewa ba su da wata hujjar da za su nemi kotu ta umarci INEC ta sake zaɓe ko kuma ta ƙwace nasarar da su ka yi ta bai wa Atiku da PDP ba.
Babban Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun, ya ce zargin da Atiku ke yi na wai an ƙi bin Dokar Zaɓe ta 2022, ba shi da tushe, dalili ko hujja.
Tinubu kamar yadda lauyan sa ya shaida wa kotu, “ba tilas ba ne don INEC ta ce za ta aika sakamakon zaɓe daga BVAS zuwa iReV a ce tilas sai ta yi hakan a dukkan Rumfunan Zaɓe 176,974 na ƙasar nan.
Idan ba a manta ba, kafin zaɓe INEC ta ce za ta aika sakamakon zaɓe daga Na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Zaɓe BVAS, zuwa Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta iReV, domin duk jama’a daga ko’ina su gani. Sai dai kuma INEC ba ta yi hakan zaɓen shugaban ƙasa ba..
Shi dai Atiku ya lissafa wa kotu laifukan karya ƙa’idar zaɓe har 12 da ya ce an yi a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.
Daga cikin su akwai: Danne haƙƙin masu zaɓe, yi wa ƙuri’u da akwatinan zaɓe asarƙala, dagula lissafin alƙaluman BVAS, dagula tsarin tantance masu jefa ƙuri’a, dagula tsarin tattara ƙuri’u, kai har ma da kayan zaɓe da yanayin rarraba kayan zaɓen duk an sa ha’inci a ciki, don a taimaki APC a daƙile PDP.
A na sa ɓangaren, lauyan Tinubu ya ce ƙarar da Atiku ya shigar fa arankatakaf ya na ƙorafi ne kan rashin tattara sakamakon zaɓe daga BVAS zuwa iReV da INEC ba ta yi ba, bayan tun kafin a yi zaɓe ta bada tabbacin za ta yi hakan. “To ai “tabbaci” ta bayar, rashin yin hakan saboda wasu dalilai kuwa ba ta karya dokar zaɓe ko ɗaya ba.” Inji lauyan Tinubu.