Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi iƙirarin cewa wani ɗan takarar gwamnan Jihar Adamawa da ba ta ambaci sunan sa ba, ya zargi jami’an ta cewa sun je Gidan Gwamnatin Jihar Adamawa sun yi ganawa a asirce .
Wanda ya yi zargin ya ce ɗan takarar ya bai wa jami’an na INEC “jerin sunayen jami’an tattara sakamakon zaɓe da Turawan Zaɓe” waɗanda aikin zaɓen ya rataya a wuyan su.
A kan haka ne INEC ta ƙaryata wannan wannan zargi da ta ce an yi wa wasu jami’an ta da ta tura aikin gudanar da zaɓen gwamna a Jihar Adamawa.
Kakakin Yaɗa Labaran INEC, kuma Kwamishinan INEC mai lura da wayar da kan masu zaɓe, Festus Okoye ne ya nesanta INEC daga wannan zargi, a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Mai zargin dai ya ƙara da cewa INEC ta zaɓi wasu jami’an zaɓe ne musamman ta tura su Adamawa ɗin don su murɗe zaɓe.
Zargin Shisshigin INEC A Zaɓen Adamawa Ƙarya Ce – Okoye:
“Mu na tabbatar da cewa maganar zargin wai wasu jami’an INEC sun je Gidan Gwamnatin Adamawa an yi taron sirri da su, ko zargin bayar da sunayen jami’an zaɓe, duk ba gaskiya ba ce,” inji Okoye.
“Ai irin wannan taron ganawar ya ba zai yiwu ba, domin jami’an mu sun rigaya sun yi rantsuwar kama aiki da gaskiya, yin aiki da gaskiya, da kuma tsare aiki da gaskiya.”
Okoye ya ce INEC ta naɗa wa Adamawa Baturen Zaɓe tun kafin zaɓen Shugaban Ƙasa, wanda aka naɗa wa zaben shugaban ƙasa, shi ne dai ya kasance Baturen Zaɓen Gwamna.
Ya ce a zaɓukan da ba a kammala a Adamawa ba, har rumfunan zaɓe 69, an tura Kwamishinonin Zaɓe 2. Amma a jihar Kebbi mai rumfuna 142, sai aka tura Kwamishinonin Zaɓe uku.
“Amma a jihohin Sokoto, Zamfara, Imo, Ribas da Ogun, duk Baturen Zaɓe ɗaya aka tura wa kowace daga cikin su.
Tuni dai INEC ta nemi Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alƙali cewa ya gaggauta sa a kama Kwamishinan Zaɓe na Adamawa, Hudu Ari, kuma a hukunta shi, sanadiyyar dagula zaɓen Adamawa da ya yi.
Discussion about this post