Ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na Labour Party, Datti Baba Ahmed ya gargaɗi shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban jojin Najeriya da su tabbata ba a rantsar da Tinubu ba shugaban Najeriya a 29 ga Mayu.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin nasarar da Bola Tinubu yayi a zaɓen shugaban kasa da aka gudanar a Najeriya a cikin Faburairu.
Tinubu ya lallasa abokan takarar sa na PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na LP wanda Dattinke wa mataimaki.
Tun bayan sanar da sakamakon zaɓen jam’iyyun PDP da na LP suka ku amincewa da sakamakon zaɓen inda suka lashi takobin kalubalantar zaɓen a kotu.
Bayan haka dukkan su su biyun musammamn su rika fitowa suna cewa su ne suka lashe zaɓen ba Tinubu ba.
A hira da Datti yayi da Talabijin din Channels ranar 22 ga Maris, ya gargaɗi shugaban kasa da babban jojin Najeriya kada su kuskura su rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya a cewar sa wai bai cancanta ba.
” Idan aka kuskura aka rantsar da Tinubu, ina tabbatar muku cewa shikenan dimokuraɗiyya ta zama gawa a Najeriya, ta mutu kenan. Kuma ba za mu yarda da haka ba.
Datti ya kara da cewa ba za su bari a gurgunta dimokuraɗiyyar a kasar nan ba da hanyar rantsar da wanda bai cancanta ba.
NBC ta hukunta Channels TV
Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai, NBC ta hukunta kamfanin talbijin na Channels ta hanyar biyan tarar naira miliyan 5 bisa laifin karya dokar hukumar.
NBC ta ce Channels TV ya karya dokar kyale wasu na amfani da tashoshin suna faɗin zantuttukan da za su iya tada zaune tsaye a kasar nan.
Kalaman da Datti ya yi sune dalilin da ya sa aka saka wa Channels wannan tara.