Shugaban hukumar Haji ta Kasa Zikirullahi Hassan ya bayyana cewa a bana maniyyaci zai biya akalla naira miliyan 3 kuɗin kujerar haji daya.
Wannan sanar wa tare da bayanin yadda farashin ya ke kamar yadda ya banbanta daga jihohin kasar ya fito daga hukumar ne a ranar Juma’a.
Maniyyatan da za su tashi daga Yola Jihar Adamawa da Maiduguri Jihar Barno, za su biya naira N2,8000,000. Wadanda za su ta shi da ga sauran jihohin yankin Arewacin Najeriya kuma za su biya naira N2,919,000.
Maniyyata daga jihar Edo za su biya naira N2,968,000.00 sannan na jihohin Ekiti da Ondo za su biya N2,980,000.000
Maniyyata daga jihar Cross River za su biya naira N2,943,000.00, na jihar Osun za su biya N2,983,000.00. Maniyyata daga jihohin Legas, Ogun da Oyo za su biya naira miliyan 3 babu naira , wato N2,999,000.000.
Sannan kuma maniyyata daga yankin kudu mao kudu da na kudu maso gabashin Najeriya, za su biya naira N2,968,000.00