Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi fatali da neman belin da Tukur Mamu ya shigar ta hannun lauyan sa.
An kama Tukur Mamu watanni bakwai da su ka gabata, dangane da hannun da ake zargin ya na da shi wajen kusanci ko alaƙa da ‘yan ta’addar da su ka kai hari kan jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna.
Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ce iƙirarin da aka yi cewa Mamu ba shi da lafiya, ba gamsassun dalilan da kotu za ta iya amincewa ba ne har ta bayar da belin wanda ake tuhuma da laifin da ya danganci ta’addanci.
An kama Mamu bisa zargin kusanci da ‘yan ta’addar da su ka kai hari kan jirgin ƙasa a ranar 27 Ga Maris, 2022 tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
Mutum takwas ya mutu a nan take a lokacin kai harin, yayin da aka yi garkuwa da mutum 168.
An riƙa sakin mutanen bayan an riƙa biyan maƙudan kuɗaɗe, yayin da sauran 23 da su ka daɗe ba a saki ba, su ka shaƙi iskar ‘yanci watanni shida bayan su na tsare.
An sake su ranar 5 Ga Oktoba, 2022 bayan Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani.
Mamu wanda ake zargin shi ke karɓo kuɗin fansa daga hannun iyalan waɗanda ke hannun ‘yan ta’adda ya na kai masu, an kama shi ne a filin jirgin Cairo, babban birnin Masar kan hanyar ta zuwa Saudi Arebiya.
Gwamnatin Najeriya ce ta sa ‘Yan Sandan Ƙasa da Ƙasa su ka kamo mata shi a ranar 6 Ga Satumba, 2022.
A lokacin da ya ke tsare a Cairo, SSS sun yi dirar mikiya a gidan sa da ke Kaduna.
Bayan sun yi bincike, sun bayyana samun kayan sojoji a gidan sa da kuɗi. Sun kuma binciki ofishin sa tatas.
Ana tuhumar Mamu da laifuka 10, waɗanda duk ya ƙi yarda ya aikata.