Hedikwatar Tsaron Najeriya ta bayyana kiraye-kirayen neman a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da wasu ke yi cewa irin gwamnatin da su ke magana fa haramtacciyar gwamnati ce.
Hedikwatar ta kuma bayyana cewa abin takaici ne ganin yadda wai har wasu ke fatan a ƙafa gwamnatin riƙon ƙwara.
Kakakin Yaɗa Labaran Hedikwatar Tsaro, Musa Ɗanmadami ne ya sanar da haka yayin taron ganawa da manemanta labarai a ranar, ranar Alhamis.
Ɗanmadami wanda Manjo Janar ne, “Na sha ji da ganin haƙilon da wasu ke yi na a kafa mulkin Gwamnatin Riƙon Ƙwarya.
“Yin magana a irin wannan magana ba aikin mu ba ne. Amma dai Gwamnantin ta Riƙon Kwarya haramtacciyar gwamnati ce .”
Ya ce ‘yan ruɗu da sharri ne kawai zai nemi a yi gwamnatin riƙon ƙwarya.
Tsokaci: Gwamnatin Riƙon Riƙon Ƙwarya Ko Ihun-ka-banza!
A ranar Laraba ce Hukumar Tsaro ta SSS ta bayyana cewa ta bankaɗo ƙoƙarin da wasu gantalallu ke yi, domin su ingiza a jingine kwansitushin don a kafa Gwamnatin Riƙon Ƙwarya a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Hukumar, Peter Afunanya ya fitar, ya ce sun magano waɗanda ke ƙulla maƙarƙashiyar, amma dai bai bayyana sunayen ko wane ne ba. Amma kuma sanarwar ta ce za su daƙile ƙoƙarin na su.
“Wannan haramcin ba zai samu gindin zama ba, ba kuma za a amince da shi a tsarin dimokraɗiyya ba.
“Musamman kuma ganin yadda su ke ya kitsa wannan tuggu, kutunguila da algungumanci jim kaɗan bayan kammala zaɓe.
“Waɗannan masu shirya wannan maƙarƙashiya ga dimokraɗiyya, su yi taruka da dama ba sau ɗaya ba, ciki har da tsara hanyoyin da za su bi domin su cimma la’anannen burin su. Daga ciki akwai ɗaukar nauyin mummunar zanga-zanga a manyan garuruwan ƙasar nan, yadda za ta yi munin da za a kafa Dokar Ta-ɓaci.
“Wata hanya kuma da su ka ɗauka ita ce garzayawa kotu su samu umarnin haramta rantsar sabbin shugabannin da za a naɗa, ciki har ma da majalisar tarayya da na jihohi.”
Sanarwar da SSS su ka yi ta zo ne bayan ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na LP, Datti ya kada a rantsar da Tinubu a ranar 29 Ga Janairu. Dalilin sa shi ne APC ba ta samu kashi 25 bisa 100 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa a Gundumar FCT Abuja ba.
Baba-Ahmed ya misalta rantsar da Tinubu da cewa “tamkar kawo ƙarshen dimokraɗiyya ce.” Saboda haka sai ya shawarci Babban Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola kada ya rantsar da Tinubu.
A bayanin na sa, ɗan Datti ya ce “Babu zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a Najeriya”.
Cikin tattaunawar, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa “Najeriya ba ta da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
A cikin wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Litinin a Gidan Talbijin na Channels, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da kuma gargaɗi ga Cif Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola kada ma su halarci Dandalin Eagle Square wurin rantsar da Tinubu, saboda babu ma dalilin yin taron ballantana rantsarwar.
Datti ya ce taron ranar 29 Ga Mayu domin rantsar da Tinubu da Shettima haramtacce ne idan ma sun ce za su yi, saboda takarar Tinubu da ta Shettima duk haramtattu ne.
Ya ce shi dai Tinubu bai cika sharuɗɗan da doka ta gindiya ba kafin a bayyana shi wanda ya yi nasara.
“Saboda dokar ƙasa ta bayyana cewa sai ɗan takara ya ci jihohi 24 da Gundumar FCT Abuja tukunna, sannan za a ce ya ci zaɓe. Shi kuwa Tinubu bai ci FCT Abuja ɗin ba.
Daga nan ya yi wa Cif Jojin Najeriya jan-hankalin cewa kada shiga shirgin rantsar da Tinubu da Shettima, domin haramtattun ‘yan takara ne.
Ya ce INEC ce ta yi shirme da gangancin bayyana bayyana Tinubu da Shettima waɗanda su ka yi nasara, alhali ba su yi ɗin ba, sannan kuma takarar su haramtacciya ce, har aka yi gangancin damƙa masu satifiket na lashe zaɓe.
“Karya doka ce a rantsar da wanda bai cika sharuɗɗan dokar cin zaɓe ba. Yin hakan tamkar komawa ce a mulkin soja. Duk wanda ya rantsar da wanda bai cancanta ba, ya karya doka. Kuma ba su cancanta zama shugabanni ba.” Cewar Datti.
Ya ce tuni ya daina tunanin adalci a kotun Najeriya, tun daga lokacin da Kotun Ƙoli ta bai wa Sanata Ahmad Lawan takarar sanata, alhali kuwa ya karya doka.
“Doka ta hana ɗan takara fitowa takara fiye da ɗaya a lokaci guda. Amma Sanata Lawan ya fito takarar shugaban ƙasa, kuma ya fito takarar sanata duk a lokaci guda. Wannan kuwa ya karya doka.
“Ni da farko ai na fito takarar sanata a Kaduna, amma da aka ce na fito takarar mataimakin shugaban ƙasa, sai na janye takarar sanatan da na je yi.” Inji Datti.
Dama kuma tun kafin a kammala ƙirga ƙuri’u, sai da PDP da LP su ka nemi a daina, saboda zargin INEC ta karya ƙa’ida, ba ta aika sakamakon zaɓe cikin Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe daga Na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Zaɓe (BVAS).
Haka shi ma tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci INEC ta dakatar da tattara sakamakon zaɓe, a sake sabon zaɓe kawai.
Amma Fadar Shugaban Ƙasa ta yi biris da Obasanjo, ta ce Buhari ba zai tsoma baki a harkokin INEC ba, domin zaman kan ta ta ke yi.
Zanga-zanga A Majalisar Tarayya:
Kwana kaɗan kafin SSS su fitar da sanarwar ta, wasu tsiraru sun yi zanga-zanga zuwa Majalisar Tarayya, su na kira a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya. Daga nan kuma su ka zarce Hukumar Tsaron Ƙasa ta Sojoji ɗungurugum, su na roƙon sojoji su karbey gwamnati kawai.
To dama wannan kiraye-kirayen an daɗe ana yin sa tun kafin zaɓen 2023.
Kwanaki kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasa, Daraktan Kamfen ɗin TInubu, a ɓangaren yaɗa labarai, Femi Fani-Kayode ya ja hankalin cewa, wasu na ƙoƙarin yi wa zaɓen 2023 ƙafar ungulu, su na a a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.
Lamarin ya harzuƙa SSS, har su ka gayyace shi, daga baya ya bada haƙuri.
Cikin watan Afrilu na 2022, Afe Babalola ya yi kiran kada a yi zaɓe, a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.
Ko kafin a yi zaɓe sai da Bola Tinubu ya yi zargin akwai masu yin maƙarƙashiyar hana a yi zaɓe, don a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya. Haka ya faɗa a Ekiti.
Shi ma Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna sai da ya nanata zargin da Tinubu ya yi.
Ko ma wace irin kitimirmira ake ƙullawa, wannan baƙar aniyar ta masu neman kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, irin wadda aka yi a 1993, ba za ta yiwu a yanzu ba. Sun makara, aniyar su ta bi su.