Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun Juma’a 7 da Litinin 10 ga Afrilu hutun Easter.
Babban sakataren ma’aikatar aiyukkan cikin gida Shuaib Belgore ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Belgore ya ce ministan ma’aikatar aiyukkan cikin gida Rauf Aregbesola ya sanar da haka a madadin gwamnatin tarayya.
Aregbesola ya yi kira ga Kiristoci da su rika yin koyi da halayan da Yesu Almasihu da ya yi a lokacin yana duniya wato zaman lafiya, yafiya j, hakuri, kaunan juna da sauran su.
Ya Kuma yi kira a gare su da su Yi amfani da wannan lokaci na Easter domin yin addu’o’I saboda tabarbarewar rashin tsaro a kasan.
Aregbesola ya kara yin kira ga ‘yan Najeriya da bakin dake zama a kasar da su zama masu kiyaye doka tare da mara wa jami’an tsaro baya wajen ganin an samar da zaman lafiya a kasan.
Ya fadi haka ne gabanin mika mulkin kasa da za a yi a watan Mayu mai zuwa da sa ran cewa za a yi taron mika mulki cikin kwanciyar hankali kamar yadda aka yi a 2019..
Discussion about this post