Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Kogi, Muktar Bajeh, ya sauka daga muƙamin sa domin nuna fushi kan yadda Gwamna Yahaya Bello na jihar ya kira shi da sunan ɗan ta’adda.
Ba Honorabul Bajeh kaɗai ne Yahaya Bello ya kira ɗan ta’adda ba, har da wasu sauran ‘yan majalisar dokokin jihar su takwas, duk ya kira su ‘yan ta’adda.
Ranar 23 Ga Maris ce Bello ya kira su ‘yan ta’adda, su tara saboda rawar da su ka taka a Zaɓen ‘Yan Majalisar Dokokin Kogi a ranar 18 Ga Maris, 2023.
Cikin wasiƙar da Gwamna Bello ya aika wa Kakakin Majalisar Jiha, Matthew Kolawole, ya umarce shi ya dakatar da ‘yan majalisar guda 9, tare da neman a binciki abubuwan da su ka yi a lokacin zaɓe.
To amma shi Bajeh, a wasiƙar da ya aika wa Majalisa, ya ce zai ajiye muƙamin Shugaban Masu Rinjaye ne domin ya nuna rashin amincewa kan yadda majalisar ta koma raƙumi da aka a hannun gwamna Bello.
“Ina sanar da ajiye muƙami na. Ba ni da sauran sha’awar kasancewa shugaban ku. Daga yanzu na yi murabus.” Inji shi a cikin wasiƙar da ya aika.
Bayan Kakakin Majalisa ya karanta wasiƙar, sai Honarabul Alfa Momoh-Rabiu ya nemi a nemi a naɗa Bulaliyar Majalisa Ahmed Ɗahiru ya maye gurbin Bajeh. Kuma hakan aka yi, majalisa ta amince.
Discussion about this post