Zuwa yanzu dai akwai ‘yan takarar zaɓen shugaban ƙasa da kuma jam’iyyu shida da su ka garzaya kotu, su na jayayya kan nasarar da Bola Tinubu ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ya samu a zaɓen 25 ga Fabrairu.
Masu ƙorafin na ƙoƙarin ganin cewa kotu ta hana rantsar da shi a ranar 29 Ga Mayu.
A cikin ‘yan takarar, Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na LP duk su na iƙirarin su su ka ci zaɓe. Kowa na cewa shi ya kamata a bai wa nasara. A cikin sauran masu jayayyar kuma akwai mai cewa a bai wa Atiku domin shi ya yi na biyu.
Na baya-bayan nan da ya fito kuma, wato Ambrose Owuru, wanda ya yi takarar shugabancin ƙasa a 2019, ya ce shi ya kamata a rantsar ba Tinubu ba, domin har yau Kotun Ƙoli ba ta yanke hukuncin ƙarar da ya shigar da Buhari tun cikin 2019 ba.
A taƙaice dukkan su dai ƙoƙarin su shi ne kada a rantsar da Tinubu a ranar 28 ga Mayu, lamarin da mai karatu zai yi wa ƙararrakin karatun ta-natsu har ya tantance abu mai yiwuwa ko maras yiwuwa. Musamman ganin cewa shari’a mace ce da ciki, ba a san abin da za ta haifa ba.
Bajekolin Jam’iyyu Da ‘Yan Takara Masu Jayayya Da Tinubu A Kotu:
Yayin da PDP, LP, AA da kuma APM duk su ka garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara kan rashin amincewa da nasarar APC da ɗan takarar ta Bola Tinubu a zaɓen 2023, jam’iyya ta cikon biyar mai suna APP (All Peoples Party) ta bi sahun su, ita ma ta garzaya kotu, inda ta ke jayayya da nasarar da Bola Tinubu da APC zu ka yi, ta zaɓen shugaban ƙasa ba 2023.
Ɗan takarar APP mai suna Osita dai ya samu ƙuri’u 12,839, yayin da Tinubu ya samu miliyan 8.8, Atiku da ya zo na biyu, ya damu miliyan 6.9.
Shi kuma Peter Obi na LP ya samu miliyan 6.1.
Bayan ya bayyana yadda aka yi maguɗi a na sa zargin, Osita ya buga misalai a wurare daban-daban, sannan kuma ya kawo wasu dalilan da ya ce hujja ce mai nuna cewa Bola Tinubu bai cancanci fitowa takarar zaɓen ba ma baki ɗaya.
Daga cikin dalilan ko hujjojin sa, ya ce an yi tashe-tashen hankula a wasu yankuna, wasu wurare da dama kuma ba a yi zaɓen ba ma ɗungurugum.
APP ta ce zaɓen 2023 bai cika sharuɗɗan da Dokar Zaɓe ta 2022 ta gindaya ba.
Haka kuma a cewar sa, INEC ba ta tura sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a cikin Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta iReV daga cikin na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Katin Zaɓe ba.
Ya ce a fam-fam ɗin da Tinubu ya cike na INEC, babu takamaiman sunayen garuruwan da ya yi karatu ko inda makarantun su ke
Cikin makon jiya ne jam’iyyyar Action Alliance (AA) ta ce wa kotu a soke nasarar da INEC ta ce APC da Tinubu su ka yi, a sake zaɓe.
Jam’iyyar ‘Action Alliance’ (AA), ta bi sahun PDP, LP da APM, inda ita ma ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana rashin amincewa da nasarar da APC da ɗan takarar ta, Bola Tinubu su ka yi na lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu.
AA ta roƙi kotu a sake zaɓe saboda INEC ba ta loda sunan haƙiƙanin ɗan takarar ta na Shugaban Ƙasa ba, Solomon David-Okanigbuan a manhajar hukumar zaɓen ba.
AA dai ta shigar da ƙara a ranar 16 Ga Maris, cewa duk da kotu ta bai wa INEC umarnin ta saka sunan halastaccen ɗan takarar ta na shugaban ƙasa, wanda hakan ya janyo wa jam”iyyar ta su asarar ƙuri’u masu yawan gaske.
Lauyan AA da Okanigbuan mai suna Dauda Usman, ya nemi a jingine zaɓen nasarar zaɓen da Tinubu ya samu, a sake wani sabo.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa an samu ƙarin jam’iyyar da ke jayayya da nasarar Tinubu, inda ta ce Asiwaju bai cancanci takara ba, a ƙwace a bai wa Atiku Abubakar na PDP.
Jam’iyyar ‘All Peoples Movement’ (APM), ta ce takarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC da ya yi nasara, haramtacciya ce, domin ba a bi ƙa’iba wajen zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Tinubu, wato Kashim Shettima.
APM ta bi sahun su PDP da LP, ta maka APC da INEC ƙara ranar 20 Ga Maris, ta na so Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe a Abuja ta bayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda ya zo na biyu, cewa shi ne ya yi nasara, kuma shi ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ba Tinubu ba.
A ranar 1 Ga Maris ne aka bayyana cewa Tinubu ya yi nasara.
A cikin kwafen takardun ƙarar da APM ta shigar, ya ce Tinubu bai shiga takara bisa ƙa’ida ba, saboda Kashim Shettima bai cancanci tsayawa takara ba.
Idan ba a manta ba, lokacin da Tinubu ya fito takara, ya miƙa sunan Ibrahim Masari a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Ibrahim Masari ɗan Katsina ne, jihar Shugaba Muhammadu Buhari. An ajiye shi ne matsayin ɗan takarar wucin gadi, kafin zaɓen mataimaki, wanda aka ɗauki Shettima daga baya.
Masu sharhin siyasa maganin Tinubu ya ɗauki Ibrahim Masari ne don cika umarnin INEC cewa ranar 27 Ga Yuni ce za ta rufe karɓar sunayen ‘yantakara, wato ranar 17 Ga Yuni, 2022.
A ranar 10 ga Janairu Ibrahim Masari ya janye, Aka maida sunan Shettima.
A Daura Tinubu ya bayyana sunan Shettima matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, yayin da ya kai wa Buhari ziyasa.
A kan haka ne APM ta ce Shettima ya fito takara a wurare biyu, wato takarar sanata da ta mataimakin shugaban ƙasa a lokaci guda.
“Har zuwa ranar 25 ga Yuli, 2022, akwai sunan Tinubu a cikin masu takarar sanatoci.”
APM ta ce ta samu kwafen takarda daga INEC a ranar 14 Ga Yuli cewa a ranar an canja sunan Ibrahim, aka maye gurbin sa da na Ibrahim.
APM ta ce Sashe na 131(C) da 142 ya nuna Ibrahim Masari ne ɗan takarar mataimakin Tinubu, tunda ya janye kuwa, takarar Tinubu ta faɗi kenan.
APM ta ce Sashe na 131(C) da 142 na doka ya nuna Tinubu ba ɗan takara ba ne, domin ba ya halatta ya tsaya takara ba da mataimaki ba.
Waɗannan da wasu dalilai ne ya sa APM ta nemi kotu ta kwace nasara daga hannun Tinubu ta bai wa Atiku Abubakar na PDP da ya zo na biyu.
29 Ga Mayu: Ni Ya Kamata A Rantsar, Ba Tinubu Ba – Ambrose, Ɗan Takarar 2019:
Tsohon ɗan takarar jam’iyyar HDP a zaɓen shugaban ƙasa, Ambrose Owuru, ya nemi Kotun Ɗaukaka Ƙara kada ta bari a rantsar da Bola Tinubu matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 Ga Mayu.
Wannan ƙara da Ambrose na HDP ya shigar, ita ce ƙara ta shida da jam’iyyu da ‘yan takara daban-daban su ka shigar su na nuna rashin amincewa da nasarar Bola Tinubu na APC.
Sai dai su waɗancan biyar ɗin, sun maka Bola Tinubu ƙara ce a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, shi kuwa Ambrose a Kotun Ɗaukaka Ƙara ya kai ta sa ƙarar.
Daga cikin waɗanda su ka maka Tinubu ƙara kotu, akwai PDP da Atiku Abubakar, LP da Peter Obi.
A ƙara mai lamba CA/CV/259/2023 wadda Ambrose ya shigar, ya nemi a dakatar da rantsar da Bola Tinubu. Kuma a cikin waɗanda ya ke ƙara, ya haɗa har da Shugaba Muhammadu Buhari da Antoni Janar Abubakar Malami da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
Ambrose Owuru wanda lauya ne, ya yi takara tun a zaɓen 2019 a ƙarƙashin HDP, kuma ya sha kaye a hannun Buhari, amma sai ya yi iƙirarin cewa shi ne ya yi nasara.
A kan haka ne Ambrose Owuru ya haƙiƙice cewa shi ne ya yi nasara, amma aka ba Buhari.
Don haka ya ce wa kotu Tinubu ba zai yiwu ya zama shugaban ƙasa ba a 2023, har sai an rantsar da shi Ambrose ɗin ya yi shekaru huɗu na zangon sa tukunna.
Hujjar Da Ambrose Owuru Ke Taƙama Da Ita:
Ya ce, “Shugabancin Muhammadu Buhari na 2019 zuwa 2023 haramtacce ne, domin an rantsar da shi alhali Kotun Ƙoli ba ta yanke hukuncin ƙarar Buhari da ya shigar kan zaɓen Buhari ba.
Saboda haka ya nemi kotu ta hana “miƙa mulki daga hannun Buhari zuwa hannun Bola Tinubu a ranar 29 Ga Mayu. Sannan kuma ta hana rantsar da Tinubu ɗin, saboda Kotun Ƙoli ba ya yanke hukuncin ƙarar zaɓen Buhari da ya kai tun cikin 2019 ba.”
Lauyan Ambrose Owuru mai suna Odion Peter, ya roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta gaggauta yanke hukuncin ƙarar da ya shigar kafin ranar rantsarwa.
Discussion about this post