Tantagaryar fitinannen ɗan ta’addan da ya fitini yankin Tsafe da wasu ƙauyukan Jihar Katsina, Ado Aleru, ya sako mutum 74 daga cikin mutane 91 da ya yi garkuwa da su daga ƙauyen Wanzamai.
Mutanen dai sun kwashe kwanaki har 22 a cikin daji, kafin a tara kuɗaɗen da za a karɓo fansar su.
An sake su ranar Juma’a bayan an biya masu kuɗaɗen fansa.
Daga majiya ƙwaƙƙwara dai PREMIUM TIMES ta ji daga bakin ɗaya cikin waɗanda aka yi tattaunawar sako da mutanen 74 cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu, waɗanda su ka yi ƙoƙarin tserewa daga inda su ke a tsare.
Majiya ta ce da farko su sun ma yi tunanin mutum 84 ne aka arce da su, ashe ma har sun kai 91. Yayin da su kuma ‘yan sandan jihar Zamfara su ka ce mutum 9 kaɗai aka yi garkuwa da, iƙirarin da ya ɓata wa mazauna ƙauyen Wanzamai rai matuƙa.
Dukkan mutanen 74 da aka saki dai an kwantar da su Asibitin Tsafe da na Wanzamai, saboda sun koma gida a yanƙwane.
PREMIUM TIMES ta bayar da labarin yadda aka yi garkuwa da mutanen a ranar 7 Ga Afrilu.
Yadda Aka Karɓo Su A Hannun ‘Yan Bindiga:
Ko da aka arce da mutanen, dai sauran jama’ar gari su ka riƙa buga wayoyin wasu gaggan ɓarayin yankin. A ƙarshe dai su ka tabbatar Ado Aleru ne ya yi garkuwa da su.
“A ƙarshe dai ya bugo ya ce su na hannun sa. Sannan kuma ya nemi abubuwa da dama da ya ke so a yi masa, kafin ya sake su. Cikin abin da ya ke so, ya zarge mu da laifin taimaka wa sojoji su na kashe yaran sa.
Aleru dai ya nemi su sa a cire sojojin da aka girke, amma su ka ce ba za su iya yin haka ba.
“Ya nemi kuɗi, kuma mu ka je gida mu ka riƙa neman yadda zamu tara abin da za mu iya tarawa mu kai masa.
“Mu ka ce kowa ya kawo Naira 30,000, inda da kyar mu ka tara Naira miliyan 3 da kyar.
“Da aka kai masa kuɗin, sai ya haɗa mu da yaran sa ya je mu je mu sallame su. Miliyan 3 da mu ka kai kuwa, ya riƙe su a matsayin kuɗin yaran sa huɗu sa sojoji su ka kashe da kuma baburan sa huɗu da sojoji su ka ƙwace bayan sun kashe yaran na na Aleru huɗu.”
Bayan sun koma gida ne sun sake tara naira milyan 3 su ka kai, washegari aka kira su aka su je su tafi da waɗanda ake tsare ɗin.
“Da mu ka je sai mu ka ga mutum 74 ya saki daga cikin 91sauran kuma na hannun sa. Ya ce sai an ƙara kai kuɗin fansa.”
A yanzu dai su na tunanin idan sun ƙara sayar da gonaki su ka kai masa kuɗin, zai iya sakin sauran.
Labarin Yadda Aka Yi Garkuwa Da Mutum 91:
Mazauna garin Wanzamai sun fitar da sunayen mutum 85, bayan ‘yan sanda sun ce mutum 9 kaɗai aka arce da su.
Mazauna ƙauyen Wanzamai da ke cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, sun fito da jerin sunayen mutum 85 da su ka tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun tafi da su cikin daji, sun yi garkuwa da su a ranar Juma’a.
‘Yan ƙauyen na Wanzamai sun fito da sunayen ne domin su ƙaryata Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, wadda ta ce mutum 9 ne kaɗai aka yi garkuwa da su.
Wani mazaunin garin Tsafe mai suna Haruna Bashar, ya ce waɗanda aka yi awon-gaba da su ɗin ‘yan ƙauyukan Wanzamai da Kucheri ne a Jihar Zamfara da kuma wasu ƙauyukan yankin ‘Yankara a Jihar Katsina.
“Ni yanzu haka a gidan mu akwai fiye da mutum biyar waɗanda su ka gudo daga Wanzamai, su na zaman gudun hijira nan cikin gidan mu.
“Mutane da a tsorace su ke, da yawan su ma sun gudu daga kauyen. Ba mu san yawan waɗanda aka kama ba, saboda a cikin dazuka ma sun kakkama wasu da dama.
“Na ji ma sun kama mutane a Kucheri da Yankara.”
Wata majiya kuma a ƙauyen Wanzamai da ta nemi a ɓoye sunan ta ce an yi garkuwa da mutum 85, kuma an yi garkuwa da wasu a Kucheri duk a ranar.
“Ƙwarai, takardar da ka gani mai ɗauke da sunayen mutum 85 da aka yi garkuwa da su, ba bogi ba ce, daga ƙauyen mu ta fito. Saboda haka duk wani jami’in ɗan sandan da ya ce wai mutum 9 kaɗai aka sace, to ya zo ƙauyen mu a nuna masa hujjar cewa mutum 85 ne.” Inji majiyar.
Mazauna Wanzamai sun ce waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin sun haɗa har da waɗanda aka kama cikin daji, lokacin da su ka je ɗebo itace, waɗanda su ka tafi sassabe a gonakin su.
Sai dai Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Zamfara Mohammed Shehu ya ce bayanin da su ka samu ya nuna cewa mutum 9 kaɗai aka arce da su.
Discussion about this post