Mazauna ƙauyen Wanzamai da ke cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, sun fito da jerin sunayen mutum 85 da su ka tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun tafi da su cikin daji, sun yi garkuwa da su a ranar Juma’a.
‘Yan ƙauyen na Wanzamai sun fito da sunayen ne domin su ƙaryata Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, wadda ta ce mutum 9 ne kaɗai aka yi garkuwa da su.
Wani mazaunin garin Tsafe mai suna Haruna Bashar, ya ce waɗanda aka yi awon-gaba da su ɗin ‘yan ƙauyukan Wanzamai da Kucheri ne a Jihar Zamfara da kuma wasu ƙauyukan yankin ‘Yankara a Jihar Katsina.
“Ni yanzu haka a gidan mu akwai fiye da mutum biyar waɗanda su ka gudo daga Wanzamai, su na zaman gudun hijira nan cikin gidan mu.
“Mutane da a tsorace su ke, da yawan su ma sun gudu daga kauyen. Ba mu san yawan waɗanda aka kama ba, saboda a cikin dazuka ma sun kakkama wasu da dama.
“Na ji ma sun kama mutane a Kucheri da Yankara.”
Wata majiya kuma a ƙauyen Wanzamai da ta nemi a ɓoye sunan ta ce an yi garkuwa da mutum 85, kuma an yi garkuwa da wasu a Kucheri duk a ranar.
“Ƙwarai, takardar da ka gani mai ɗauke da sunayen mutum 85 da aka yi garkuwa da su, ba bogi ba ce, daga ƙauyen mu ta fito. Saboda haka duk wani jami’in ɗan sandan da ya ce wai mutum 9 kaɗai aka sace, to ya zo ƙauyen mu a nuna masa hujjar cewa mutum 85 ne.” Inji majiyar.
Mazauna Wanzamai sun ce waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin sun haɗa har da waɗanda aka kama cikin daji, lokacin da su ka je ɗebo itace, waɗanda su ka tafi sassabe a gonakin su.
Sai dai Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Zamfara Mohammed Shehu ya ce bayanin da su ka samu ya nuna cewa mutum 9 kaɗai aka arce da su.
Discussion about this post