Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Alƙali Usman wasiƙa cewa ya gaggauta sa a kama Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Farfesa Hudu Ari.
CIkin wata sanarwa da INEC ta fitar bayan tashi taron gaggawa a ranar Talata, 18 ga Afrilu, hukumar zaɓen ta kuma rubuta wa Sakataren Gwamnatin Tarayya wasiƙar sanar da shi cewa ya sanar da hukumar da ta dace irin babbar ɓarna da kasassaɓar da Hudu Ari ya tafka, domin su san irin matakin da za su ɗauka a kan sa.
Haka nan kuma INEC ta bada umarnin a ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a lokacin da Baturen Zaɓe na Jihar Adamawa ya kimtsa sosai.
A na ta ɓangaren, tuni Binani ta garzaya kotu, ta na neman a hana INEC haramta nasarar da Kwamishinan Zaɓe Ari ya bayyana ta yi.
‘Yar takarar gwamnan Adamawa a ƙarƙashin APC, Aisha Binani, ta garzaya kotu, ta nemi a hana INEC haramta nasarar lashe zaɓen gwamna da Kwamishinan Zaɓe na Adamawa, Farfesa Hudu Ari ya yi azarɓaɓin bayyana cewa ita ce ta yi nasara.
Kwamishinan Zaɓen Adamawa, Farfesa Hudu Ari ne ya bayyana sunan ta a matsayin wadda ta kayar da Gwamna Ahmadu Pintiri na PDP.
Binani na fatan ganin ta kayar da gwamna mai ci yanzu, Ahmadu Fintiri, wanda ya fi ta samun yawan ƙuri’u a zaɓen ranar 18 ga Maris.
Kwamishinan Zaɓen Adamawa Hudu Ari, ya yi azarɓaɓi, giringiɗishin ayyana Binani ta yi nasara, alhalin ba aikin sa ba ne bayyana sakamakon zaɓen.
Tuni dai INEC ta hana Ari zuwa ofishin ta da ke Adamawa, kuma an umarci ya kai kan sa Hedikwata a Abuja.
Binani ta shaida wa kotu cewa bayan Ari ya bayyana ta yi nasara, PDP ta tayar da hankalin jama’a, har magoya bayan ta su ka kai wa Kwamishinan Zaɓe hari.
Binani ta ce INEC ba ta da ikon soke nasarar da Kwamishinan Zaɓe ya ce ta yi, sai dai Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe ce kaɗai za ta iya yin haka.
Lauyan Binani mai suna Hussaini Zakariya’u (SAN), ya ce gyararren kundin dokokin INEC ya bai wa kotu ikon soke wani hukunci da INEC ta ɗauka.
Tuni dai ita kuma PDP ta nemi a garƙame Kwamishinan Zaɓen Adamawa, a koya masa hankali.
Jam’iyyar PDP ta yi kakkausan kiran a gaggauta kama Kwamishinan INEC na Jihar Adamawa, Hudu Ari, wanda ya bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar tun kafin a kammala tattara sakamkon zaɓe.
Cikin wata sanarwa da Kakakin PDP, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Lahadi, ya yi kira ga Sufeto Janar Alƙali Usman-Baba cewa ya umarci ‘yan sanda su gaggauta kama Ari tare da gaggauta gurfanar da shi a kotu, kuma a zartas masa da hukunci daidai gagarimin laifin da ya tafka.
Masu sa-ido da ejan-ejan sun tabbatar cewa Ari ya bayyana sakamakon tun kafin a kammala tattara sakamakon.
Sannan kuma baya ga cewa ba shi ne Dokar Zaɓe ta halasta wa sanar da sakamkon zaɓe ba, ya yi kasassaɓar bayyana sakamako a lokacin da Baturen Zaɓe AA Zuru da haƙƙin bayyana sakamakon ke kan sa ba ya ɗakin bayyana sakamakon.
Tuni dai masu sharhin siyasa ke cewa muddin ba a ɗaure masu aikata laifukan zaɓe, dimokraɗiyyar Najeriya za ta ci gaba da samun cikas daga tasgaron da ta ke samu yayin gudanar da zaɓe.
Idan ba a manta ba, a ranar Lahadi ce INEC ta yi fatali da sanarwar nasarar da Kwamishinan Zaɓe ya yi giringiɗishin cewa Binani ta APC ta yi, ta gayyaci Baturen Zaɓe da Kwamishina zuwa Abuja.
Hedikwatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi fatali da gaggawar bayyana sakamakon nasarar da Kwamishinan Zaɓen Adamawa ya ce Aishatu Binani ta yi.
Baturen Zaɓe dai ya yi azarɓaɓin sanar da cewa Binani ceta yi nasara, duk kuwa ba a kammala ƙidaya ba. Sannan kuma bashi ne wajibcin bayyana sakamakon zaɓe ya rataya a hannun sa ba.
“Azarɓaɓin da Kwamishinan Zaɓe na INEC na Jihar Adamawa ya yi ya bayyana nasarar wani ko wata ‘yar takara, ba abin amincewa ba ne. Saboda ba aikin sa ba ne, kuma ba a kammala haɗa ƙidaya ba.
“Saboda haka INEC na sanar da Baturen Zaɓe na Adamawa shi da Kwamishinan Zaɓe na jihar su gaggauta kawo kan su Hedikwatar INEC a Abuja, da gaggawa ana nan su.”
Sanarwar wadda Kwamishinan Wayar da Kai na INEC, Festus Okoye ya fitar a ranar Lahadi, kuma ta na ɗauke da bayanin sanarwar cewa Hukumar Zaɓe ta dakatar da komai wanda ya danganci sanarwar sakamakon zaɓen Jihar Adamawa.”
Safiyar Lahadi ne jaridar Daily Trust ta buga labarin cewa Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa Hudu Yunusa Ari, ya bayyana Aishatu Ɗahiru da aka fi sani da Binani cewa ita ce ta lashe zaɓen gwamnan Jihar Adamawa.
Kafin nan, an dakatar da tattara sakamakon zaɓe cikin dare jiya Asabar, aka ce sai washegari ƙarfe 10 na safiya, sai Kwamishinan Zaɓe ya bayyana cewa Binani ta APC ce ta yi nasara.
Ari ya yi wannan gangaci a lokacin da shi Baturen Zaɓe ba ya nan.
Sanarwar dai ta janyo ka-ce-na-ce a ɗakin tattara sakamakon zaɓen, cikin Adamawa da ƙasa baki ɗaya.
PDP ta nuna rashin amincewar ta ganin Kwamishina ne ya yi sanarwar, ba Baturen Zaɓe (R.O) ba.
Mele Lamiɗo wanda shi ne Baturen Zaɓe, ba ya cikin ɗakin tattara sakamakon zaɓen a lokacin da aka yi sanarwar.
Idan ba’a manta ba, tun a lokacin tattara sakamakon zaɓen da INEC ta ce bai kammalu ba na ranar 18 Ga Maris, sai da PDP ta yi ƙorafin cewa ba ta yarda ba kuma ba ta yi amanna da Haruna Ari ba.
A na su ɓangaren, tuni APC a Adamawa ta fara murnar nasara, kafin Hedikwatar INEC ta Ƙasa ta yi fatali da sanarwar.
Discussion about this post