Farashin kayan abinci da sauran na masarufi ya tashi sama zuwa kashi 22.4 bisa 100.
Idan za a tuna, cikin watan Maris sai da tsadar rayuwa ta kai kashi 24.46, a Fabrairu kuwa ta kai kashi 24.35.
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, NBS wadda mallakar gwamnatin tarayya ce ta bayyana wannan hali da tattalin arziki ke ciki a ranar Asabar.
An shiga wannan tarangahuma ce tun bayan da Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeriya, CBN su ka karɓe kuɗaɗe a hannun jama’a bayan an fito da sabbin da ba su wadata ba.
Shirye-shiryen Rage Wa Talakawa Miliyan 50 Raɗaɗin Ciwon Cire Tallafi:
A farkon makon jiya ne Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ciwo bashin Dala Miliyan 800, don ta raba wa faƙirai miliyan 50 kuɗin tausar-ƙirjin fargabar tsadar rayuwa, idan an cire tallafin fetur daga watan Yuni.
Alamomi daga Gwamnatin Tarayya sun nuna tabbas marasa galihu za su ɗanɗana kuɗar tsadar rayuwa daga watan Yuni zuwa ‘illa ma sha-Allahu’, yayin da an kammala shirin janye tallafin fetur, lamarin da zai sa tsadar sa ta sa da yawan masu motocin hawa za a jingine ababen zirga-zirgar na su, saboda tsadar fetur.
Dalilin haka ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta fara kinkimo bashin Dala Miliyan 800 daga Bankin Duniya, domin ta raba wa marasa galihu ‘yar la’adar tausaya masu dangane da mawuyacin halin rayuwar da za au afka nan gaba daga watan, idan an cire tallafin fetur.
Bashin wanda babu ruwa a ciki, wato a Turance ‘World Bank Facility’, za a raba kuɗaɗen ne ta hanyar tuttura wa marasa galihu miliyan har su Miliyan 50, domin a rage masu raɗaɗin ƙuncin rayuwar da za su afka nan gaba kaɗan.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa da Fadar Shugaban Ƙasa, ranar Laraba, a Abuja.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron.
Zainab ta ce za a fara raba wa talakawa ta hanyar tuttura masu a asusun bankunan su, amma sai bayan an cire tallafin a watan Yuni tukunna.
Ta ce wannan Dala Miliyan 800 ba ita kaɗai ce za a raba masu ba, akwai sauran wani bashin ya na tafe, wannan somin-taɓi ne kawai.
Ta ce tuni akwai rajistar gidajen faƙirai, matalauta da marasa galihu har miliyan 10, waɗanda ta kintata yawan jama’ar da ke cikin lissafin ƙididdigar za su kai mutum miliyan 50. Ta ce waɗannan adadin duk sunayen su na cikin Rajistar Tattara Ƙidayar Marasa Galihu ta Ƙasa.
Zainab ta ce gwamnati a shirye ta ke ta rage wa marasa galihu raɗaɗin tsadar rayuwar da za su fuskanta nan gaba, ta wasu hanyoyi ba sai ta hanyar tura masu kuɗaɗen cefane ta asusun ajiyar su na bankuna ba.
“Ƙungiyar Ƙwadago ma akwai yiwuwar ta shigo da tsarin sayen motocin sufuri masu yawan gaske, domin rage wa ma’aikata da marasa galihu tsadar kuɗin mota nan da ɗan wani lokaci idan an janye tallafin fetur.
Sauƙi Da Sarƙaƙiyar Da Ke Tattare Da Bashin:
Akwai sauƙi da sarƙaƙiyar da ke tattare da bashin dala miliyan 800, wanda Najeriya ta ciwo don rage raɗaɗin tsadar fetur idan an cire tallafin mai kwanan nan.
1. A ƙarƙashin bashin wanda aka ciwo a Bankin Duniya, an ƙulla yarjejeniya tsakanin Najeriya cewa ƙungiyar ƙasashe na IDA ce za ta bayar da kuɗaɗen. Ƙungiya ce mai bayar da tallafin lamuni ga matalautan ƙasashe, ba tare da ta caje su kuɗin ruwa masu yawa ba.
2. USAID ta ce bashin ba ya tayar da hankalin matalautan ƙasashe, domin kuɗin ruwan da ake ɗorawa, ba su taka kara ya karye ba.
3. Kuma shi wannan bashin zai ɗauki shekaru masu yawa ana biya da kaɗan kaɗan, ba irin bashin da ake riƙa biya duk wata ba ne.
3. An dai sa hannun yarjejeniyar tsakanin Najeriya da IDA tun a ranar 16 Ga Agusta, 2022.
4. Za a raba kuɗaɗen ne ga mabuƙata da ke cikin lungunan karkara da garuruwa da birane, ta hanyar tura wa faƙirai da talakawa a asusun ajiyar su na banki.
5. Kuɗin tamkar tausar-ƙirji ne Gwamnatin Tarayya za ta yi wa mai rabon samun kuɗaɗen, saboda nan da watanni biyu masu zuwa za a janye tallafin fetur a ƙarshen watan Yuni, lamarin da zai sa fetur ya yi tsadar da bai taɓa yi ba a gidajen mai a baya.
6. Najeriya za ta riƙa biyan kuɗin ruwa kashi 0.5 duk shekara, sai harajin kashi 0.75 na ladar jeƙala-jeƙalar bada kuɗaɗen lamunin, sai kuma shi ma a duk shekara. Sai kuma wasu kashi 1.25 da za ta riƙa biya duk shekara matsayin harajin ganin ‘alat’ na kuɗaɗen a cikin Asusun Gwamnatin Najeriya.
7. Za a riƙa biyan kuɗaɗen duk bayan watanni shida, wato za a riƙa biya a duk ranakun 15 Ga Janairu da 15 Ga Yuli na kowace shekara.
8. Sai narar 15 Ga Janairu za a fara biyan bashin, a kammala biya nan da shekaru 24 da fara biya. Domin za a fara biya ne a cikin 2027, a kammala biya ranar 15 Ga Yuli, 2051.
9. Za a riƙa biyan kuɗaɗen da Dalar Amurka, ba da naira ko ɗanyen man fetur ba.
10. Ranar da za a fara biya, Najeriya za ta biya kashi 1.65 na kuɗaɗen da ta ramto. Ranar biyan ƙarshe kuma za ta biya kashi 3.40 na sauran kuɗaɗen da za su kasance su ne su ka rage ba a biya ba.
11. Daga ranar 16 Ga Agusta da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar, to idan aka yi kwanaki 120 a jere, Najeriya ba za ta iya fasa karɓar lamunin ba, ko ta so, ko ta ƙi. Haka IDA mai bayar da bashin ba zai fasa bayarwa ba.
Matsayi Da Malejin Bashi A Ruwan Cikin Najeriya:
Zuwa Satumba, 2022 dai Babbar Daraktar Kula da Ofishin Basussuka na Najeriya, Patience Oniha, ta ce ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 44.06.
Kenan gwamnati mai hawa kan mulki nan da 29 ga Mayu, za ta gaji bashin Naira tiriliyan 77 idan aka yi bin-diddigin halin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ke ciki.
Discussion about this post