Fadar Shugaban Ƙasa ta yi raddi kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke, wadda ta umarci Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta maida Ifeanyi Ararume kan muƙamin sa na Shugaban NNPCL.
A cikin gajeren bayanin da fadar ta yi, ta ce Ofishin Antoni Janar kuma Ministan Shari’a zai ɗaukaka ƙarar wannan hukunci da Kotun Tarayya ta yanke.
“To har yanzu dai Ofishin Ministan Harkokin Shari’a bai kai ga samun kwafe ɗin hukuncin da kotun ta yanke.
“Shugaban Ƙasa dai ya na da cikakken yaƙinin cewa za a bi matakan da shari’a ta gindiya, kuma NNPCL ya fara shirye-shiryen ɗaukaka ƙara.” Haka Kakakin Shugaban Ƙasa, Femi Adesina ya bayyana a cikin gajeren rubutun da ya fitar a ranar Talata.
Babbar Kotun dai ta umarci a biya Ararume haƙƙin diyyar Naira biliyan 5, saboda cire shi da Shugaba Buhari ya yi, a tsari wanda kotu ta ce haramtacce ne.
Ararume ya ce bai san an cire ba har sai ranar rantsar da shugabannin NNPCL, inda aka ambaci sunan wanda ana naɗa a madadin sa, cikin Janairu, 2022.
Cikin Nuwamba dai kotu ta yanke hukuncin cewa a maida Ararume kan muƙamin sa, kuma Buhari ya ƙi amincewa da diyyar naira biliyan 100 da Ararume ya nemi ya biya shi a kotu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ba ta da hurumin da za ta saurari ƙarar da tsohon sanata Ifeanyi Ararume ya maka shi a kotun, inda mai ƙarar ya nemi Buhari ya biya shi diyyar naira biliyan 100, saboda ya soke naɗin da ya yi masa na Shugaba Maras Cikakken Iko a kamfanin NNPCL.
A sanarwar ƙin amincewa da hurumin kotun, wadda Ofishin Antoni Janar na Tarayya ya shigar a madadin Buhari, ta ce Buhari ya cire Ararume bayan ya naɗa shi, saboda a matsayin Buhari na ma’aikacin gwamnati, Sashe na 251 na Dokar Najeriya ta 1999 ta ba shi ikon naɗawa da tsigewa.
Maimuma Shiru wadda ita ce Daraktar Riƙo ta Sashen Shigar da Ƙararraki a Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ce ta sa wa sanarwar hannu kuma aka gabatar wa kotun.
Hujjar da Maimuma Shiru ta bayar a madadin Buhari, ta ce an shigar da ƙarar watanni bayan wa’adin da Dokar Kare Martabar Aikin Gwamnati ta 2004, ta bayar ya daɗe da wucewa.
Shiru ta ce an tsige Ararume tun a ranar 17 Ga Janairu 2022, shi kuma bai kai ƙara ba sai bayan watanni bakwai da cire shi, wato a ranar 12 Ga Satumba 2022.
Buhari ya ce a ƙarar sa da aka shigar an ƙi bin matakan da shari’a ta tanadar, don haka kotun ba ta da hurumin sauraren ƙarar.
A ranar 8 Ga Disamba ne Buhari ya aika wa Babbar Kotun Tarayya ta Abuja wannan wasiƙar rashin amincewar ta ta saurari ƙarar.
A cikin watan Nuwamba dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Ifeanyi Ararume ya rarumi Buhari zuwa kotu, saboda ya janye naɗin shugabancin NNPCL da ya yi masa.
Sanata Ifeanyi Ararume ya maka Shugaba Muhammadu Buhari kotu, saboda shugaban ƙasa ya janye takardar shaidar naɗa shi shugaban NNPCL marar cikakken iko da Buhari ɗin ya yi.
An dai naɗa Ararume cikin Satumba 2021, amma sai ana cire sunan sa tun kafin a rantsar da mambonin hukumar gudanarwar NNPCL ɗin a cikin January, 2022.
Jin haushin haka sai Ararume wanda Sanata ne a jihar Imo, ya garzaya Babbar Kotun Tarayya ta Imo a ranar 12 Ga Satumba, 2022 ya maka Buhari kotu, inda ya ƙalubalanci cirewar da aka yi masa watanni takwas baya.
Ya shaida wa kotu ce an cire shi ba bisa ƙa’idar da ya kamata a cire shi ba. Ya ce an janyo masa rikicewar ayyukan ofishin sa.
Ararume ya ce cire shi an karya Doka Kamfanoni ta CAMA 2021 da kuma dokar Harkokin Fetur (PIA) ta 2021.
Ya roƙi kotu cewa sai a biya shi diyyar Naira biliyan 100, sannan kuma kotu ta bayar da umarnin cewa a maida kan muƙamin sa da aka naɗa shi da farko na Shugaban Kwamitin Hukumar NNPCL wanda aka cire shi tun kafin ya shiga ofis.
Sannan kuma ya roƙi kotu ta soke du wani aiki ko wani umarni da Hukumar NNPCL ta yi tun daga ranar da aka naɗa mata shugabannin hukumar gudanarwa zuwa yau.
Discussion about this post