Rundunar ƴan sandan jihar Gombe sun damke wani mai suna Adamu Baje dake da shekaru 30 sannan kuma da ya shahara wajen yin garkuwa da mutane a jihar.
Kakakin rundunar Mahid Mu’azu ya sanar da haka da yake gabatar da wanda aka kama ranar Alhamis.
Mu’azu ya ce ‘yan sanda sun kama Baje bayan ya yi garkuwa da wasu mutane biyu Fatsuma Buba da Manu Adamu a garin Nafada dake karamar hukumar Nafada.
Ya ce rundunar ta samu labarin garkuwar ne bayan Wani Alhaji Adamu Bello mazaunin kauyen Labe ya kai kara a ofishin ‘yan sanda dake karamar hukumar Nafada.
“Bello ya ce wasu mahara sun shiga kauyen dauke da bindigogi da adduna suka afka gidansa dake kauyen Labe a karamar hukumar Nafada inda suka ji musu rauni sannan suka yi garkuwa da Fatsuma Buba da Manu Adamu.
“Bayan haka ne ƴan sanda tare da mafarauta suka fantsama domin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.
“ Ƴan sandan sun kwace shanu 7, jakukuna 4, tumakai 19, awaki 10, wayar Techno daya da dai sauransu.
Kakakin rundunar ya ce an aika da mutanen da aka ceto asibiti likitoci na duba su.
Mu’azu ya ce rundunar ta kama wasu mutane biyu Joshua Dogo mai shekaru 27 da Mu’azu Abdullahi mai shekaru 22 dauke da bindiga kirar pistol da wuka sun kwace wa wani Abubakar Usman mai shekara 18 babur a Garin Barde dake karamar hukumar Kwami.
Ya ce ‘yan sandan dake aiki a Tunfure ne suka kama Dogo da Abdullahi ɗauke da bindiga, wuka da babur din da suka sace.
“Rundunar na neman Salisu Ahmed-Yahaya, Murtala Mohammed, Adamu Dodo, Abba Euro da Adamu Harka ruwa a jallo bayan sun kai wa wani Abdullahi Mohammed hari a shagonsa dake cikin kasuwa.
” Waɗannan mutane sun sassare Abdullahi da gariyo sannan suka ji masa ciwo da wukake, kafin suka kwace naira 200,000 da wurin sa.
Mu’azu ya ce idan suka kammala bincike za su kai mutanen da aka kama kotu domin a yanke musu hukunci.
Discussion about this post