Sojin Najeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun kama wami mutum dake harkallar makamai a karamar hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro na jihar Samuel Aruwan ya sanar da haka wa manema labarai ranar Alhamis.
Aruwan ya ce dakarun sun kama Aminu Abdullahi dauke da makamai a Polwire dake karamar hukumar Birnin Gwari.
“Dakarun sun kama Abdullahi a dalilin bayanan siri da suka samu game da safarar bindigogi da yake yi.
“Dakarun sun kama wani mota kirar Toyota Corolla dankare da harsasai har 2,000 da aka boye a wurare daban-daban a cikin motar.
“A cikin motar dakarun sun kama harsasai masu tsawon 7.62mm 1,079, jigidar harsasai 886, harsasai da ake kira tracer guda 139.
Aruwan ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya yaba wa kokarin da jami’an tsaron suka yi wajen samar da tsaro a jihar.
Ya yi kira ga jami’an tsaro su zage damtse wajen ganin sun samar da tsaro a jihar da Najeriya baki daya.
Bayan haka a ranar Laraba rundunar sojin sama a karkashin ‘Operation Whirl Punch’ sun yi wa wasu mahara ruwan bama-bamai a Birnin Gwari.
Kafin dakarun su darkakesu maharan sun kai hari a kauyen Sabon Layi dake Birnin Gwari.
Dakarun sun kashe mahara da dama a wannan hari.