Lai Mohammed, wanda shi ne ministan yada labarai na gwamnatin mai barin gado, ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, da tada hankalin jama’a kan sakamakon zaben shugaban kasa, yana mai cewa cin amanar kasa ne abin da yake yi.
Obi ya zo na uku a zaben shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga watan Faburairu wanda Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki ya lashe. Shi Obi da Atiku Abubakar da ya zo na biyu, suna kalubalantar sakamakon zaben a kotu, inda suka ce zaben da kuma sakamakon zaben ba abin da mutane suka zaba bane aka bayyana. Dukkan yan takarrar biyu sun fito fili sun yi kira ga magoya bayansu da su guji tashin hankali yayin da suke kalubalantar sakamakon a kotu.
Sai dai kuma musamman magoya bayan Obi sun ci gaba da nuka bacin ran su bisa ga sakamakon zaben suna masu cewa suna nan a bakan su na dole a dakatar da rantsar da Bola tinubu shugaban kasa ranar 29 ga Mayu.
” Bai kamata a ce wai Obi da mataimakin sa Datti su rika furta kalaman da su tada hankalin yan Najeriya ba, su rika cewa idan aka rantsar da Tinubu Dimokuradiyya a Najeriya ta zama gawa ba.
“Irin kalaman da Obi ke furtawa kalamai ne na mutumin da ya sha kayi. Amma A ina ake baiwa wanda ya zo na uku shugabanci bayan ga na daya da na biyu idan ba Obi da makarraban sa sun zauce ba.
A karshe Lai Mohammed ya ce ya ziyarci Amurka ne domin ya wayar musu da kai game da karerayin da suke ji suke kuma yadawa game da zaben Najeriya.
Mafi yawa daga cikin yan Najeriya sun amince cewa zaben 2023 ya fi zabukan da aka ta ba yi a Najeriya tun 1999.
Discussion about this post