Tsohuwar Shugabar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, Hadiza Bala, ta bayyana dalilan da su ka sa ta ƙi yi wa tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi kyauta don taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.
Rashin bayar da kyautar ce Hadiza ta bayyana matsayin ɗaya daga cikin dalilan da Amaechi ya cire ta daga Hukumar NPA, hukumar da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Sufurin Jiragen Ruwa.
Da ta ke magana a lokacin ƙaddamar da littafin ta mai suna, “Stepping on Toes – my odyssey at the Nigerian Ports Authority’ a ranar Asabar, Hadiza ta ce ba gaba da gaba ya shaida mata hakan ba. Amma dai ta ce ya riƙa shaida wa mutanen da su ka je don su ji dalilin da ya sa ya ke son durƙusar da ni ne. Shi ne ta ce ya ke shaida masu cewa babban laifi na wai ban yi masa kyautar komai ba.
“Akwai ɗabi’a a cikin manyan ma’aikatan gwamnati, wai idan wani babba a hukuma ko ma’aikata zai yi murnar zagayowar ranar haihuwar sa, idan ba ka taya shi murna ba, to wai ba ka da kirki, kuma wai ba ka nuna biyayya kenan.
“To a haka sai ma’aikata su ka ginu a kan wannan mummunar ɗabi’a, duk lokacin da ogan ku zai yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa, to sai ka sai masa kyauta. To don me zan sai masa kyautar zagayowar ranar haihuwar sa? Kuma don me za mu ci gaba da riƙo da wannan mummunar ɗabi’a?”
Ta ce, “don haka sai shi Amaechi zai ce hakan ba daidai ba ne.”
Ta ce za ta so karanta littafin da Amaechi ya ce shi ma zai wallafa, kasancewa ya yi gwamna shekaru takwas, ya yi minista, ya yi daraktan kamfen na ɗan takarar shugaban ƙasa da sauran su.
“Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na ɗaya daga cikin hukumomi 13 da ke ƙarƙashin Amaechi a lokacin da ya ke Ministan Sufuri. Ba na jin zai ƙasƙantar da kan sa, ya cika littafin da rubutu kan littafin Hadiza.” Inji ta.
Farkon fitowar littafin a satin farko na watan Afrilu, wannan jarida ta wannan jarida ta yi nazarin littafin, inda ta tsakuro wasu dalilan da su ka sa Amaechi ya yi silar cire Hadiza daga Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa.
A cikin littafin dai, tsohuwar Babbar Daraktar Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, Hadiza Bala Usman, ta fitar da littafin da ta wallafa, wanda a cikin sa ta bayyana rikita-rikitar da ta kai har aka cire ta daga shugabancin hukumar a cikin 2021.
A cikin littafin mai suna “Stepping on Toes: Aiki Na a Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa”, Hadiza ta zargi tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da kitsa silar cire ta daga ofis, cikin Fabrairu, 2022, saboda kawai ta ƙi riƙa yi masa ihisani da alfarmar da bai cancanta ba bisa ƙa’ida.
An dakatar da Hadiza tun cikin Mayu 2021, saboda Amaechi ya yi zargin ta kasa saka kuɗaɗen harajin tashoshin jiragen ruwa har Naira biliyan 165 a Asusun Tara Harajin Gwamnatin Tarayya.
Bayan dakatar da ita, Amaechi ya kafa kwamitin bincike, wanda ya shafe watanni 9 ya na aiki, amma ba a kama Hadiza da laifin ƙin zuba kuɗin haraji a Asusun Gwamnatin Tarayya ba. Sai dai kuma duk da haka, Buhari bai maida ta kan muƙamin ta ba.
Hadiza ta ce Ameachi ya ce ba ya son aiki da ita a NPA, saboda haka ko dai ta kama gaban ta ko kuma ta je kotu kawai ta ƙalubalanci dakatarwar da ya yi mata.
“Amaechi ya shaida wa wani mutum da ya yi ƙoƙarin sasanta mu cewa wai na cika son kai na, wai ban yi masa alfarmar komai a Hukumar NPA ba, kuma wai ko kyautar alfarma ta murnar zagayowar ranar haihuwar sa ban yi masa ba.” Inji Hadiza.
Akwai zarge-zarge da dama kan Amaechi a cikin littafin, wanda a na sa ɓangaren ya ce idan ya kammala karance shi kakaf, zai maida martani dalla-dalla.
Discussion about this post