Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da ɗage shirin ƙidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023, wadda tun farko aka shirya yin sa daga 3-7 ga Mayu 2023, zuwa ranar da gwamnati mai zuwa za ta saka.
Shugaban ya amince da hakan ne bayan ganawa da wasu mambobin majalisar zartarwa ta tarayya da kuma shugaban hukumar kidaya ta kasa da tawagarsa a fadar shugaban kasa a Abuja a ranar Juma’a 28 ga Afrilu, 2023.
Taron ya nanata muhimmancin gudanar da kidayar jama’a da gidaje, shekaru 17 bayan da aka yi irin haka a Najeriya. Hakan zai ba da dama sanin yawan jama’a da ke kasar nan da tattara sahihan bayanai da za su samar da manufofin ci gaban kasar nan, da inganta rayuwar al’ummar Najeriya.
Ya kuma yaba wa tsarin da hukumar ke bi wajen gudanar da sahihin kidayar jama’a, musamman yadda aka yi amfani da dimbin fasahar zamani domin aiwatar da aikin kidayar.
Tuni dai kafin dage wannan aiki na kidayar jama’a, hukumar ta dauki ma’aikatan wucin gadi, sannan kuma an siyo na’urori na zamani domin aikin kidayar.
Babban dalilin da wasu ke ganin shine ya sa aka dage shirin yanzu ya haɗa da shirin mika mulki ga sabuwar gwamnati da za a yi nan da kwanaki 29 masu zuwa.
Wani mai yin sharhi akan al’amuran kasar nan, Yunusa Lawal, da ya tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA, ya bayyana cewa ” akwai matsaloli da za samu idan har aka ce za a cigaba da aikin kidayar jama’a ganin yadda shirye shiryen miƙa mulki ga sabuwar gwamnati ya matso kusa-kusa yanzu.
” Da mika mulki za a ji ko da aikin kidayar jama’a, wannan sabuwar babi ce za a buɗe a Najeriya, an yi matukar yin hangen nesa akai, idan sabuwar gwamnati ta natsa sai ta duba ta gani ta gyara tsarin sai a yi ƙidayar.” Inji Lawal