Shugaban kamfanin Facebook wanda sune ma su mallakin manhajar WhatsApp ya bayyana cewa daga ranar Talata na wannan mako, za a iya amfani da da lamba ɗaya don buɗe Whatsapp har a wayoyi hudu.
Mark Zuckerberg, ya ce daga yanzu za a iya amfani da manhajar WhatsApp wanda aka bude a akan waya sannan a buɗe shi a wata wayar da lambar guda ba tare da ka buɗe wata ba.
A baya kafin wannan sanarwar, dole sai dai mai amfani da manhajar WhatsApp ya buɗe a kan waya ɗaya ne. Idan ka nemi buɗe ta awata yawar sai ka rasa wacce ta ke buɗe a wayarka ta farko, domin da kansa zai ce ba za ka iya haka ba sai dai ko dai ka fice daga waccan ko kuma ka hakura da wannan.
Wannan ci gaba zai ba mutane daman su buɗe WhatsApp din a wayoyin su kuma suna amfani da shi ba tare da dole sai a waya daya ba ko kuma sai sun buɗe wata sabuwar asusun WhatsApp ɗin.
Discussion about this post