Yayin da PDP, LP, AA da kuma APM duk su ka garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara kan rashin amincewa da nasarar APC da ɗan takarar ta Bola Tinubu a zaɓen 2023, jam’iyya ta cikon biyar mai suna APP (All Peoples Party) ta bi sahun su, ita ma ta garzaya kotu, inda ta ke jayayya da nasarar da Bola Tinubu da APC zu ka yi, ta zaɓen shugaban ƙasa ba 2023.
Ɗan takarar APP mai suna Osita dai ya samu ƙuri’u 12,839, yayin da Tinubu ya samu miliyan 8.8, Atiku da ya zo na biyu, ya damu miliyan 6.9.
Shi kuma Peter Obi na LP ya samu miliyan 6.1.
Bayan ya bayyana yadda aka yi maguɗi a na sa zargin, Osita ya buga misalai a wurare daban-daban, sannan kuma ya kawo wasu dalilan da ya ce hujja ce mai nuna cewa Bola Tinubu bai cancanci fitowa takarar zaɓen ba ma baki ɗaya.
Daga cikin dalilan ko hujjojin sa, ya ce an yi tashe-tashen hankula a wasu yankuna, wasu wurare da dama kuma ba a yi zaɓen ba ma ɗungurugum.
APP ta ce zaɓen 2023 bai cika sharuɗɗan da Dokar Zaɓe ta 2022 ta gindaya ba.
Haka kuma a cewar sa, INEC ba ta tura sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a cikin Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta iReV daga cikin na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Katin Zaɓe ba.
Ya ce a fam-fam ɗin da Tinubu ya cike na INEC, babu takamaiman sunayen garuruwan da ya yi karatu ko inda makarantun su ke
Cikin makon jiya ne jam’iyyyar Action Alliance (AA) ta ce wa kotu a soke nasarar da INEC ta ce APC da Tinubu su ka yi, a sake zaɓe.
Jam’iyyar ‘Action Alliance’ (AA), ta bi sahun PDP, LP da APM, inda ita ma ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana rashin amincewa da nasarar da APC da ɗan takarar ta, Bola Tinubu su ka yi na lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu.
AA ta roƙi kotu a sake zaɓe saboda INEC ba ta loda sunan haƙiƙanin ɗan takarar ta na Shugaban Ƙasa ba, Solomon David-Okanigbuan a manhajar hukumar zaɓen ba.
AA dai ta shigar da ƙara a ranar 16 Ga Maris, cewa duk da kotu ta bai wa INEC umarnin ta saka sunan halastaccen ɗan takarar ta na shugaban ƙasa, wanda hakan ya janyo wa jam”iyyar ta su asarar ƙuri’u masu yawan gaske.
Lauyan AA da Okanigbuan mai suna Dauda Usman, ya nemi a jingine zaɓen nasarar zaɓen da Tinubu ya samu, a sake wani sabo.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa an samu ƙarin jam’iyyar da ke jayayya da nasarar Tinubu, inda ta ce Asiwaju bai cancanci takara ba, a ƙwace a bai wa Atiku Abubakar na PDP.
Jam’iyyar ‘All Peoples Movement’ (APM), ta ce takarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC da ya yi nasara, haramtacciya ce, domin ba a bi ƙa’iba wajen zaɓen ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na Tinubu, wato Kashim Shettima.
APM ta bi sahun su PDP da LP, ta maka APC da INEC ƙara ranar 20 Ga Maris, ta na so Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe a Abuja ta bayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda ya zo na biyu, cewa shi ne ya yi nasara, kuma shi ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, ba Tinubu ba.
A ranar 1 Ga Maris ne aka bayyana cewa Tinubu ya yi nasara.
Discussion about this post