Ministan yada Labarai Lai Mohammed ya bayyana cewa da gangar hukumar Zabe ta ke saka sakamakon zabe a manhajar iReV a lokacin zabe kuma dalilan sun hada da yadda masu kutse na yanar gizo suka yi ta kokarin dagula sakamakon zaben da canja alkaluman zaben.
Lai ya bayyana wa jaridun Kasar Amurka cewa abinda aka fadi musu suke ruwaitowa karyar banza ce da labaran kanzon kurege.
Lai ya ce ” A lokacin da hukumar zabe ke kokarin saka sakamakon zaben da ake samu kai tsaye daga mazabu sai kwararrun injiniyoyin hukumar su ka gano kutse da ake kokarin yi cikin manhajar domin dagula sakamakon zaben da kuma kokarin canja alkaluman zaben.
” A wannan lokaci ne hukumar ta dakatar da aikin haka sannan ta umarci ma’aikatanta su cikaba da dakile wannan farmaki da ake kawo wa manhajar sannan su gaggauta kirkirar wata da za ci gaba da saka sakamakon zaben.
” Da yake rufunar zaben ne masu yawa a kasar kuma ba a lokaci guda ake samun sakamakon zabukan ba, dole lokacin da za a sakasu su banbanta.
” Duk da haka dokar kasa ma ba ta ce sai an saka sakamakon zabe dole a manhajar iReV kafin abayyana sakamakon zabe, rashin fahimta ce da zafin faduwa kawai ya gigita sauran yan takaran da suka sha kayi a zaben.