Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa, ya bayyana cewa zai yi amfani da fasahar zamani wajen daƙile matsalar tsaro a Jihar Katsina.
Haka kuma ya ƙara da cewa zai yi amfani da mazauna lungunan yankunan karkara wajen yaƙi da ‘yan bindiga.
Raɗɗa wanda ya tattauna da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, ya je ne domin ya nuna wa Shugaba Muhammadu Buhari satifiket ɗin sa na yin nasara, a matsayin sa na zaɓaɓɓen gwamnan jihar da Buhari ya fito.
Zaɓaɓɓen gwamnan ya je ne a bisa rakiyar Gwamna Aminu Masari na jihar.
Ya ce matsalar tsaron da ke damun jihar ta Shugaban Ƙasa ce zai fi bai wa fifiko da muhimmanci da zarar an rantsar da shi.
Raɗɗa dai shi ne tsohon Daraktan Hukumar Bunƙasa Ƙanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEDAN) ta Ƙasa).
Ya ce idan babu tsaro mazauna jihar zai zama zuwa gonaki, makarantu da kasuwanni da sauran harkokin inganta tattalin arziki duk sun gagare su.
“Na sha faɗa cewa magance matsalar tsaro ce zan fi bai wa muhimmanci. Saboda noma ne babbar sana’ar da ke kawo wa al’ummar jihar abin dogaro, kuma shi ne hanyar samar da aikin yi. Da noman nan akasarin jama’a su ka dogara.
“Saboda haka tilas gwamnati ta bayar da tsaro ga jama’a. To mun yi alƙawarin za mu yi amfani da mazauna lungunan karkara da kuma fasahar zamani wajen daƙile matsalar tsaro a Katsina.
Ya ce Buhari ya tunatar da shi cewa ya yi aiki tsakanin sa da Allah ba tare da nuƙu-nuƙu ba, komai komai a yi shi ƙeƙe-da-ƙeƙe, ba tare da almubazzaranci ba.
Premium Times Hausa dai ko a makon jiya ta buga labarin dalilin da Raɗɗa ya ce ba a so a riƙa kiran sa ‘His Excellency’ – Dikko Raɗɗa, Zaɓaɓɓen Gwamnan Katsina.
Ya ce zai fi so a riƙa kiran sa da “Mr Governor ko kuma Malam Dikko Raɗɗa” amma ba ya so a riƙa kiran sa da “His Excellency”, har sai bayan ya kammala wa’adin sa tukunna.
Raɗɗa ya bayyana haka a ranar Asabar a Abuja, lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai.
An zaɓi Raɗɗa a ƙarƙashin APC, ya samu ƙuri’u 859,892, ya doke Yakubu Lado na PDP, wanda ya samu ƙuri’u 486,620.
“Ni dai ba na so idan an rantsar da ni a riƙa kira na “His Excellency”, saboda kalma ce mai nuna gwamna ya cika komai, ya yi dukkan abin da ya wajaba da wanda ya kamata ya yi, da kuma nauyin da ya wajaba ya sauke.
“Amma idan za a iya kira na da His Excellency ɗin bayan na kammala wa’adi na, idan har jama’a sun ga na yi masu ayyuka masu kyau. Don haka ma har gara a riƙa kira na Mr Gobernor ya fi min sauƙi.
“Ni ina so na ji ni ina daidai da kowa, saboda ba na son ana ƙaƙaba min ‘Excellency’ ɗin nan har ana kumbura min kai. Ni zan ma fi so kawai a riƙa kira na Malam Dikko Raɗɗa.”
Idan an tuna, a 2019 ma Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas ya cire “His Excellency” a sunan sa. Haka shi ma tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, wanda ya yi mulki daga 2010 zuwa 2018, an riƙa kiran sa da “Ogbeni”, maimakon “His Excellency”.
Shi kuwa Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, ana masa laƙabi da “Arakunrin”, wato Mister kenan da kalmar Yarabanci.
Da ya ke magana kan ajandar gwamnatin sa, Raɗɗa ya ce idan aka rantsar da shi, zai fi maida hankali ne kan matsalar tsaro wadda ta addabi Jihar Katsina.
Discussion about this post