A ranar Asabar 22 ga Afrilu Sarkin Dokin Kara na Lere ya yi hawan Sallah tare da Hakimai da Dagatai na ‘Kara’ yayin da suka zazzagaya talakawansu da ke garin don gaisawa tare da yin shagulgulan Sallah Karama.
Hawan Sallar ya ƙayatar ainun fiye da shekarun baya, domin kuwa ya sami dinbin mahalarta maza da mata da suka fito daga yankunan Iyakokin Bauchi da Kano.
Shehu Sani Lere, wanda ya buga yadda bukin ya gudana da yadda ya ƙayatar a shafin sa ya ce Hawan na Kara ya fito da al’adunnmu na dauri, tare da Kara taskace tarihin Irin sana’o’inmu na iyaye da kakanni.
Matasan da suka fito daga cikin gidajen Makera da majema da masassaka da Wanzamai da Mahauta da gidan Fulani dukkansu kan fito da kayayyakin Al’ada don tunawa mutane inda aka baro.
Shagalin bukin ya samu halartar Gwamna Jihar Kaduna Mai barin Gado, Nasir El-Rufai da takwaransa da zai gaje shi, Uba Sani, a inda suka zagaya cikin motoci na alfarma don yi wa mutane ban-gajiyar zabe, tare da nuna Sabon Gwamna.
Taron ya Sami yabo daga mahalarta Taron daga mai girma Sarkin Lere da Gwamna da Kuma magajinsa.
Matasa ne suka shiga kamar na gwamna da da sarakuna, domin kwailwayon su domin kayata shagulgulan da kuma nishadantar mutane.
Discussion about this post