Buhari ya tashi zuwa Saudiyya a yau Talata, 11 Ga Afrilu domin zuwa aikin Umra.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ya bayyana cewa Buhari zai yi kwanaki takwas kafin ya dawo Najeriya a ranar 19 Ga Afrilu.
Ya ƙara da cewa wannan Umra ce za ta kasance ta ƙarshe da Shugaba Buhari zai yi a matsayin sa na Shugaban Ƙasa.
A tsawon shekaru takwas da ya yi kan mulki, Buhari ya ziyarci Saudiyya sau da dama.
Ya je ko dai aikin Hajji, ko Umra ko kuma taron shugabannin ƙasa da ƙasa.
Shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkin sa a ranar 29 Ga Mayu, ranar ce kuma za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC.
Discussion about this post