Mahaifiyar babban dan jaridan Najeriya Yusuf Ali, ta rasu. Hawau Yusuf ta ras ranar Lahadi, 23 ga Afrilu tana da shekaru 89, kamar yadda dan jaridan wanda shine, manajan editan (Arewa) na jaridar The Nation, a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook.
Marigayiyar, a cewar danta, ta rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya, watanni kaɗan zuwa cikarta shekaru 90 da haihuwa.
An yi jana’izar Hawwa Yusuf sa’o’i kadan bayan rasuwarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A ta’aziyyar da Buhari ya yi wa Yusuf Ali da sauran iyalan marigayiyar, shugaban kasan ya yi mata addu’ar Allah ya sa Aljanna ta zamo makomanta, sannan ya bai wa ƴaƴan ta hakurin jure wannan rashi da suka yi.
Haka shima zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu, a na shi sakon ya yi addu’ar Allah ya jiƙan mamaciyar ya san ya aljanna makoma, Amin.
Mutane da dama da suka taɓa yin mu’amala da mamaciyar sun bayyana cewa rashin Hajiya Hawwa rashi ne ga kowa da kowa.
” Idan ka taɓa yin mu’amula da ɗan jarida Yusuf Ali, za ka tabbatar da iri rashin da aka yi. Yusuf Ali mutum ne mai karamci da sanin yakamata, sannan gashi mai tausayi kuma hannun sa a buɗe suke wajen yin kyauta. Wanda hakan ke nuni da irin tarbiyya da irin gidan da ya fita.
” Allah ya ji kan mahaifiyar sa ya sa Aljanna ta zamo makomanta, Amin. In ji Yunusa Muhammad.
Discussion about this post