A bincike da bin diddigin alƙaluman sakamakon zaɓen shugaban kasa na jihar Ribas da PREMIUM TIMES ta yi a manhajar iReV na hukumar zaɓe ta gano cewa sakamakon zaɓen da aka saka a manhajar bai yi daidai da wanda hukunar zaɓe ta bayyana ba.
A sakamakon da hukumar zaɓe ta bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC ne ya lashe zaɓen jihar Ribas, amma kuma bisa ga sakamakon zaɓen da aka saka a manhajar iRev, manhajar tattara sakamakon zaɓe iReV.
Dan takarar LP Peter Obi, ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu a karamar hukumar Obio/Akpor ta jihar Ribas, kamar yadda sakamakon da hukumar zabe INEC ta wallafa a manhajar IReV.
Kuri’un da Obi ya samu a yankin na nuni da cewa ba Bola Tinubu na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben shugaban kasa a Ribas ba, sabanin sakamakon da INEC ta bayyana bayan zaɓen.
Sakamakon zaben karamar hukumar Obio/Akpor, kamar yadda INEC ta bayyana, ya nuna Tinubu ya samu kuri’u 80, 239, inda Obi ya samu kuri’u 3,829.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 368 yayin da Rabi’u Kwankwaso na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 161.
Daga baya aka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben. Atiku ya zo na biyu yayin da Obi ya zo na uku.
Amma nazari da bincike mai zurfi na sakamakon zaben da PREMIUM TIMES ta yi na mazabu 17 na karamar hukumar Obio/Akpor kamar yadda aka ɗora a IReV ya nuna bambanci matuka da sakamakon da INEC ta bayyana.
Bisa kididdigar mu, APC ta samu kuri’u 17, 158 yayin da jam’iyyar LP ta samu kuri’u 73,311 a wannan Karamar hukuma, Obio/Akpor wacce ke da rumfunan zabe 1,211.
Kamar a rumfar Zaɓe na Rumuorluoji Open Space, PREMIUM TIMES ta ga a wasu sakamakon zaɓen da aka saka a iReV, inda APC ta samu Kuri’u 17 sai a kara mata 2 a farko, ya koma 217, in da kuma LP ta samu irin haka sai a maida 2n farko 0. Wato maimakon 217 sai ya zama 17 kawai.
Haka aka rika yi a takardun rubuta sakamakon zaɓen da aka shigar manhajar, kuma duk da haka bayan an buga lissafi tas, Peter Obi na LP ne yayi nasara a jihar Ribas ɗin da kuri’u masu yawa , ba kamar yadda hukumar zaɓe ta bayyana ba.