Shugaba Muhammadu Buhari ya roƙi gafara da afuwa daga wajen ‘yan Najeriya, waɗanda ya ce mai yiwuwa ya yi wa ba daidai ba a lokacin da ya ke gudanar da aikin sa, a matsayin sa na shugaban da ya shafe shekaru takwas ya na mulkin dimokraɗiyya a jere, daga 2015 zuwa 2023.
Ya yi wannan neman yafiyar ce a ranar Sallar Idin Ƙaramar Sallah, a Abuja, wadda kuma ita ce sallar sa ta ƙarshe ya na kan mulki.
A ranar ta Juma’a, wadda ta rage wa Buhari Kwanaki ƙasa da 37 ya sauka daga kan mulki, Buhari ya kuma tuna irin rawar da ya taka a mulkin sa na farko lokacin da ya yi gwamna, ya yi minista zuwa shugaba na mulkin soja.
Ya yi wannan bayani ne ga mazauna Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja, waɗanda su ka kai masa gaisuwar Sallah bayan saukowa daga Idi a Abuja.
Ya bada labarin takarar sa sau uku a jere a 2003, 2007 da kuma 2011 amma bai yi nasara ba. Sai a karo na huɗu cikin 2015 ya yi nasara.
“Na tunkari ‘yan siyasa gadan-gadan, ana kayar da ni ina garzayawa kotu, har sau uku. Ban gajiya ba, sai a karo na huɗu na yi nasara, bayan sun gama yi min dariya. Ni kuma na kan ce Allah ne mai bada mulki.”
Buhari ya danganta nasarar sa a 2015 da 2019 da shigo da amfani da Katin Rajistar Zaɓe (PVC), wanda kati ne da ya magance maguɗin zaɓe matuƙar gaske.
Da ya koma kan dimokraɗiyya, Buhari ya ce dimokraɗiyya tsari ne mai kyau.
“Dimokraɗiyya tsari ne mai kyau. Domin idan na haka ba, ta yaya wani wani mutum daga wani ƙarshen lungu zai fito ya yi mulki har tsawon shekaru takwas. Ni garin mu Daura kilomita takwas ne tsakanin sa da Jamhuriyar.”
‘A Daura Zan Koma Na Yi Zama Na’ – Buhari:
Buhari ya ce zai koma Daura yayi zaman sa bayan ya kammala mulki a ranar 29 Ga Mayu.
“Har na ƙagara na kammala wa’adi na kawai na koma Daura da zama. Idan a can kuma aka cika ni da hayaniya, ana hana ni samun matsuwa, sai na tsallaka Jamhuriyar Nijar. Saboda na samu abin da na ke so na samu. Abin da kawai ya rage min, shi ne na koma Daura na yi zama na.”
“Ina roƙon dukkan waɗanda na yi wa ba daidai ba su yafe min.”
‘Na yafe wa Kanawa, Su Ma Ina Roƙon Su Yafe Min’ – Ganduje:
Cikin makon jiya ne aka nuno Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano ya na neman afuwar dukkan waɗanda ya yi wa ba daidai ba a shekaru takwas da ya yi ya na mulki.
A bidiyon, Ganduje ya yi kalamai a cikin murya mai taushi, inda ya bayyana cewa shi dai ya yafe wa kowa. Don haka ya na roƙon shi ma duk wanda ya yi wa ba daidai ba, to ya yafe masa.
Sai dai kuma Buhari da Ganduje sun sha martani daga ‘yan Najeriya, musamman talakawa, kuma matasa ‘yan soshiyal midiya.
Da yawa sun nuna yafiya da alhinin rabuwa da su biyu ɗin kan mulki. To sai dai kuma da dama sun riƙa tunatar da su irin halin ƙuncin da su ka jefa jama’a a ciki.
Da dama sun riƙa tuna wa Buhari irin masifar tsadar rayuwa da ake ciki, inda farashin kayayyaki ya nunka kuma ya sake ruɓanyawa, maimakon a ce an samu sauƙi, domin an zaɓi Buhari ne don a samu sauƙin.
Wasu kuma sun riƙa magana kan ɗimbin mutanen da ‘yan bindiga su ka kashe, su ka talauta da kuma waɗanda a yanzu haka ke tsare a hannun ‘yan bindiga.
Yayin da Buhari zai sauka daga mulki a ƙarshen watan Mayu, tuni Gwamantin Tarayya ta fara shirye-shiryen cike tallafin fetur, wanda hakan ke nuna farashin lita zai doshi Naira 500 kenan.
Buhari wanda ya hau mulki Dalar Amurka ba ta kai Naira 300 a kasuwar ‘yan canji ba, zai sauka ya bar ta wajen Naira 750.
Ya hau mulki ana kukan kuɗin aikin Hajji na naira 850,000, amma zai sauka a daidai lokacin da za a biya Naira miliyan 3 ba ‘yan canji.
Shi ma Ganduje ya sha jinjina kuma ya sha kwankwatsa a soshiyal midiya. An riƙa danganta lamarin gwamnan da rawar da ya taka a siyasa, lamurra na addini, raba filaye da sauran zarge-zargen da aka yi masa a baya.
Discussion about this post