A cikin alhini an bayyana rasuwar tsohon Mai Shari’a a Kotun Duniya, kuma tsohon Ministan Shari’a, Bola Ajibola.
CIkin wata sanarwar da babban ɗan sa Segun Ajibola ya sa wa hannu, kuma ya fitar, ya ce Ajibola ya rasu a Abeokuta, ranar Lahadi.
“Mu na baƙin ciki, jimami da alhinin rasuwar mahaifin mu Prince Bola Ajibola. Allah ya ba shi rabon aljanna, Amin.”
Ajibola wanda tsohon Ministan Harkokin Shari’a ne, ya rasu ya na da shekaru 89 a duniya. Ya rasu bayan fama da rashin lafiyar da ke da alaƙa da tsufa ko yawan shekaru. Kamar dai yadda iyalan na sa su bayyana.
Ya yi Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Ƙasa daga 1984 zuwa 1985.
Kuma ya kasance ɗaya daga cikin Kwamishinonin Hukumar Shata Kan Iyakar Eritrea da Habasha, wadda Kotun Duniya ta shirya a lokacin.
Tsakanin 1999 zuwa 2002 kuma, Ajibola ya zama Jakadan Najeriya a Birtaniya.
Shi ne ya kafa Jami’ar Cresent University a Abeokuta, da kuma ƙungiyar Musulmi ta Najeriya, IMA.
Discussion about this post