Ƙaramin Ministan Fetur, Timipre Sylva ya zama ɗan takarar APC na zaɓen gwamnan Jihar Bayelsa.
Sylva ya doke abokan karawar sa a zaɓen fidda gwani su biyar, inda ya samu ƙuri’u 52,062, a zaɓen fidda gwanin wanda aka yi a ranar Juma’a.
Shugaban Kwamitin Zaɓen Fidda Gwani na APC a Jihar Bayelsa, A.T Jibrin ne ya sanar da sakamakon zaɓen.
Joshua Machiver ya zo na biyu da ƙuri’u 2,078, Festus Danumiebi ƙuri’u 557, Maureen Etebu da ƙuri’u 1,277 sai kuma David Lyon mai 1,584. Yayin da Isikima Johnson ya samu ƙuri’u 584.
Lokacin da ya ke jawabin godiyar amincewa da nasarar da ya samu, Sylva wanda ya taɓa yin gwamnan Bayelsa zango ɗaya, ya nemi haɗin kan sauran ‘yan takarar da ya kayar domin APC ta samu nasara.
“Ina kira mu yi aiki tare mu samu nasarar lashe zaɓen gwamna a ranar 11 Ga Nuwamba.”
Sylva ya yi gwamnan Bayelsa daga 2007 zuwa 2011 a ƙarƙashin PDP.
Bayan ya koma APC ne Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa shi Ƙaramin Ministan Fetur, cikin 2015.
Ya ajiye aikin minista cikin Maris, 2022 domin ya samu damar tsayawa takarar gwamna.
Discussion about this post