Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar cewa Awwal Umar Dan takarar jami’yyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar dan majalisar dokoki na jihar Kaduna da zai wakilci mutanen Giwa ta Yamma.
Baturiyar zabe Maryam Suleiman ta sanar da sakamakon ranar Asabar bayan kammala zaɓen wucin gadi da aka yi.
Maryam ta ce bisa ga sakamakon zaben Umar ya samu kuri’u 15,603 Wanda da su ne ya kada abokin takarar sa Bello Mu’azu na jami’yyar PDP dake da kuri’u 14,897.
Idan ba a manta ba hukumar INEC a ranar 18 na Maris ta sanar da zaben mazaɓun Galadimawa da Kidandan zabukan da basu kammalu ba saboda wasu matsaloli da aka samu a wuraren.