Ana zargi da raɗe-raɗin cewa wasu ‘yan Majalisar Dattawa da Wakilai ta Ƙasa su biyu, sun dulmiya cikin ƙazamin sayen ƙuri’un mambobin su domin buƙatar su ta zama shugabannin majalisa ya tabbata.
Su biyun dai duk da ba a bayyana sunayen su ba, an tabbatar cewa duk ‘yan Jam’iyyar APC ne.
Su biyu waɗanda ɗaya na neman zama na uku a ƙarfin mulki, wato Shugaban Majalisar Dattawa da kuma ɗayan mai neman zama na huɗu, wato Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, sun shirya tsaf domin bai wa sauran ‘yan majalisa rashawar dala miliyan 1 kowanen su domin su jefa masu ƙuri’a.
Gwamnonin da zaɓa a ƙarƙashin APC ne su ka fallasa wannan gagarimar badaƙala, a cikin wata wasiƙar da su ka aika wa Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Gwamnonin APC sun shaida wa Tinubu cewa ‘yan majalisar su biyu sun tabbatar da aniyar su ta sayen ƙuri’ar kowane ɗan majalisa daga dala 500,000 zuwa dala miliyan 1.
“Mu na jin tsoron kada fa a kai ga maimaita abin da ya faru a 2015, ganin yadda ake ta zawarcin ‘yan majalisar jam’iyyun adawa.”
Wannan jarida ta ruwaito cewa Gwamnonin APC sun rubuta wa Tinubu wasiƙa dangane da batun tsarin karɓa-karɓa shugabancin Majalisar Dattawa da ta Tarayya.
Sun rubuta wa Tinubu wasiƙa bayan sun tashi daga wani taro a ranar 8 Ga Afrilu, inda su ka sanar da shi cewa waɗanda su ka ware maƙudan kuɗaɗen don su kashe wajen cuwa-cuwar sayen ƙuri’u daga sauran sanatoci da bambobi, za su yi amfani da kuɗi ne ta yadda za su tarwatsa tsarin karɓa-karɓa.
Sun ce masu takarar har sun fara zawarcin sabbin-shigowar majalisa da dubunnan daloli domin su saye su a ranar zaɓen shugabannin majalisun biyu.
Discussion about this post