Aƙalla mutum miliyan biyu marasa galihu ne su ka ci moriyar shirin Gwamnatin Tarayya na Rage Wa Marasa Galihu Raɗaɗin Talauci (National Poverty Reduction With Growth Strategy, NPRGS), a cikin shekarar 2022 da ta gabata.
Wannan bayanin adadi na cikin rahoton da ke cikin sanarwar da Kakakin Yaɗa Labaran Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, mai suna Laolu Akande ya fitar a ranar Alhamis.
Akande ya ce Kwamitin NPRGS ya yi taron sa ranar Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja, inda a wurin ne aka gabatar da rahoton shirin.
Taron dai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo ne ya shugabance shi.
An bada rahoton cewa ƙananan manoma miliyan 1.6 ne su ka ci moriyar shirin Bunƙasa Harkokin Noma Don Samar da Aiki (Agriculture for Job Plan).
“Sannan kuma wasu mutum 13,000 matasa sun samu horon dabarun sana’o’i a jihohi shida da su ka haɗa da Lagos, Ogun, Enugu, Gombe, Kaduna da Nasarawa.
“Yanzu haka ana shirye-shiryen samar da irin wannan horo ga wasu matasa 2000 a Jihar Edo.
“Haka kuma an ɗauki sama da ‘yan Najeriya 8,000 ayyukan titina a cikin yankunan karkara, a ƙarƙashin Shirin Gina Titina A Karkara. A ƙarƙashin shirin dai an gina titina 20 a cikin yankunan karkara 120.
Karamin Ministan Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare ne ya gabatar da rahoton.