Afrika ta Kudu ta ayyana cewa ta yanke shawarar ficewa daga mamba ɗin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Ƙasa da Ƙasa (ICC) a ranar Talata.
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana dalilai na rashin shimfiɗa adalci a tsakanin ƙasashen da ke cikin ƙungiyar.
“Tabbas gwamnatin jam’iyyar ANC ta ɗauki wannan matsaya cewa babu makawa ƙasar za ta fice daga ICC,” haka Ramaposa ya bayyana wa taron manema labarai, wanda ya yi tare da shi da Shugaban Finland, Sauli Niinisto, wanda ya kai ziyara Afrika ta Kudu.
Ramaposa ya ce ƙasar ta yanke shawarar ficewa daga ICC saboda bambancin da ƙungiyar ko kotun ke nunawa wajen zaɓen ƙasashen da ta ga damar hukuntawa ko ladabtarwa.
“Akwai batu wanda Amnesty International ta yi cewa Kotun ICC ta na kauda kai daga ganin laifin wasu ƙasashe shafaffu da mai, ta maida hankali kan wasu ƙasashen da shafaffu da mai ke son a hukunta.
“Saboda haka akwai buƙatar da duba zargin da Amnesty International ta yi. Sai dai duk da haka, wannan ba zai sa mu yi jinkirin ficewa daga ICC ba.” Inji Ramaposa.
Afrika ta Kudu ta yanke shawarar ficewa daga ICC, wata ɗaya bayan kotun ta bayar da sammacin kama Shugaban Rasha, Vladimir Putin da Kwamishinan Rasha mai kula da Kare Haƙƙin Ƙananan Yara.
ICC ta yi sanarwar neman a kama Putin a daidai lokacin da zai tafi Afrika ta Kudu, domin halartar taron ƙasashen BRICS, taron ƙungiyar ƙasashen na farko wanda Afrika ta ɗauki nauyi.
Duk da Afrika ta Kudu na cikin ICC, ba ta kama Putin ba kamar yadda ICC ɗin ta nemi ta yi.
A cikin 2016 haka ICC ta nemi Afrika ta Kudu ta kama tsohon Shugaban Sudan, Omar Al-Bashir, amma da ya kai ziyara ƙasar, ba ta kama shi ba.
Discussion about this post