Tun da safiya Asabar masu zaɓe suka fara tururuwa zuwa rumfunar zaɓen da aka soke zaɓukan su a zaben Maris.
Sai dai kuma babban aikin da ke gaban Binani na jam’iyyar APC shine yadda za ta iya samun kuri’un da zasu iya kada gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.
Binani na fuskantar babban aiki a yunkurinta na zama mace ta farko a Najeriya da aka zaba a matsayin gwamnan jiha, abinda ba a taba yi ba.
A halin yanzu tana biye da gwamna Fintiri da kuri’u 31,249. Sai dai a rumfunan zabe 69 da aka soke zaben, adadin wadanda suka yi rajista ya kai 42,785 yayin da katin zabe na dindindin da aka karɓa a 36,935.
Haka na nufin Binani za ta bukaci ace kusan dukka wadanda za su kada kuri’a a zaɓen su zaɓe ta ne da ke nufin sai ta ci akalla kuri’u kashi 90 na duka kuri’un kafin ta iya samun nasara a zaben.
Sai fa Binani na APC ta cinye kusan duka kuri’un da za a jefa yau ne shine za ta iya yin nasara, domin Fintiri na PDP na gaba da ita na kuri’u sama da 31,000, inda kuma ragowar kuri’un da ake jefa wa ayau 36,000 kacal, idan duka wadanda suka karbi katin zaɓen suka fito za ɓe kenan.