Abin dai da kamar wuya ace Mukhtar Betara ya samu ɗarewa kujerar shugaban majalisar wakilai ta tarayya a wannan lokaci duk da ko ya buɗe wuta wajen ganin ya samu goyon bayan ƴan majalisan don zama shugaban ta.
Mukhtar Betara, yana wakiltar Biu/Bayo/Shani da Kwaya Kusar a majalisar tarayya.
Babban abinda zai kawo wa Betara cikas a wannan lafiya da ya sa a gaba shine fitowa jiha ɗaya da yayi da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Ƴan majalisa da dama na ganin idan kwarewa za abi, toh shine ya fi cancanta ya zama kakakin majalisar tarayyar kasar a majalisa ta 10, saboda daɗewar sa a Majalisar da kuma sanin makaman aiki.
Amma kuma dadewa da kwarewa kawai ba zai yi masa tasiri ba domin dole kuma a duba siyasa da yadda za a samu haɗin kowa da kowa a wannan tafiya.
Betara na ta yawon ganawa da manyan ƴan siyasa, ciki harda ganawa da yayi da zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu domin samun goyon bayan sa.
Sai dai kuma masu bibiyar siyasar Najeriya da yin fashin baki na ganin cewa lallai akwai matukar wuya hakar Betara ya cimma ruwa.
Da farko dai shugaban kasa Musulmi ne, mataimakin sa Musulmi ne, sai kuma ace shugaban majalisar tarayya ya zama musulmi kuma daga jiha ɗaya da mataimakin shugaban kasa, dole ita kanta APC ta duba lamarin a duba wasu bangaren suma.
Wannan shine babbar ƙalubalen dake gaban Betara da wsu ke ganin da dai ya hakura da ya fi masa domin abin dai da kamar wuya.