A ranar Asabar da ta wuce an fallasa wani faifan murya, wanda ke ɗauke da wata tattaunawa tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi da kuma Shugaban Cocin ‘Living Faith’ na Duniya, David Oyedepo.
Faifan muryar dai jaridar People’s Gazette ce ta fallasa shi, wanda a cikin sa Obi ke roƙon Fasto Oyedepo ya taimake shi ya watsa saƙon sa ga Kiristocin Yankin Kudu maso Yamma da na wasu yankunan Tsakiyar Najeriya, ya na so ya sanar da su cewa su fito su zaɓi Peter Obi, domin zaɓen Obi “jihadin addini ne.”
Hakan ya nuna cewa Obi ya kira Oyedepo sun yi maganar kafin zaɓen 2023 kenan. Ga abin da faifan muryar ke ɗauke da shi a fassarar Hausa:
PETER OBI: “Daddy, ina so ka taimake ni ka yi wa mabiyan ka na Yankin Kudu maso Yamma da na Kwara, wato Kiristocin Kudu maso Yamma da na Kwara. Ka nuna masu cewa wannan (zaɓen) fa “jihadin Kiristoci ne.”
OYEDEPO: “Ni ma na yi amanna da haka ɗin. Na yarda da hakan. Na yarda hakan ya ke.”
PETER OBI: “Idan buƙata ta biya, to za ku taɓa yin da-na-sanin goyon baya na da ku ka yi ba.”
Yadda Ake Ragargazar Peter Obi Bayan Fallasa Maganar Sa Da Oyedepo:
Tun bayan fallasa muryar dai Peter Obi ke ci gaba da shan ragargaza daga masu sukar sa, su na cewa a matsayin sa na ɗan takarar shugaban ƙasa, ya maida zaɓe ƙabilanci da addini da nufin ya cimma burin zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Obi dai ya ƙaryata zargin da ake yi masa, har ya ƙalubalanci masu zargin sa cewa su kawo hujja.
Sai dai kuma alƙalami ya rigaya ya bushe, murya dai ta tabbata muryar Peter Obi ce.
Ruɗu Da Ce-ce-ku-ce Bayan Fallasa Muryar Obi Ya Na Neman Agajin ‘Jihadin Addini’ A Zaɓen 2023:
Yayin da magoya bayan Peter Obi a soshiyal midiya ke ƙaryata muryar, su na cewa ba ta Obi ɗin ba ce, sai ga shi washegari a ranar Lahadi Kakakin Kamfen ɗin LP Kenneth Okonkwo, ya tabbatar da cewa muryar Peter Obi ce, sai dai kuma ya yi wa kalaman wata fassara daban.
Jim kaɗan bayan ya tabbatar da sahihancin muryar, magoya bayan Peter Obi sun yi masa rubdugun baƙaƙen kalamai, su na zargin ya yi masu ƙafar ungulu, wato yayin da su ke ƙoƙarin nesanta Obi da muryar, shi kuma Okonkwo ya ce ta Obi ɗin ce.
A bayanan sa a shafin Tiwita, Okonkwo ya yi ƙoƙarin sauya fassarar “religious war”.
Ya ce Peter na so David Oyedepo ya watsa kiran tashi a zaɓi Peter Obi a ɓangaren ilahirin Kiristoci, saboda su ma sauran ‘yan takara sun maida yaƙin neman zaɓen tamkar jihadin addini.”
Ya zargi APC da ƙoƙarin sauya wa Peter Obi ma’anar abin da ya ke nufi zuwa ana yi masa kallon mai ruruta jihadi ta hanyar amfani da makamin ƙuri’a.
Okonkwo ya zargi APC da fara fito da jihadi a zaɓen 2023, ta hanyar fito takarar Muslim-Muslim a zaɓen shugaban ƙasa.
Sai dai kuma masu goyon bayan Obi na ganin kalaman Okonkwo ba su yi wa Obi gyara ba, maimakon haka ma ƙara dagula batun ya yi. Su kuma magoya bayan sai kawai su ka ci gaba da haƙiƙicewa cewa muryar ba ta Peter Obi ba ce.
Shi ma Shugaban Ofishin Yaɗa Labarai na Obi-Datti, Diran Onabule, ya bayyana cewa faifan muryar ƙirƙira ce wasu su ka yi don su ɓata Peter Obi. Hakan ya na nufin shi ma kamar sauran magoya bayan ogan sa, bai yarda da sahihancin muryar ba.
Zaɓen 2023 dai Tinubu ya yi amfani da addini ya samu ƙuri’un Musulmin Arewa a Muslim-Muslim, kuma Yarabanci da ‘Emi lokon’ ya samar masa ƙuri’u da yankin Kudu maso Yamma.
Obi ya yi amfani da Kiristanci ya samu ɗimbin ƙuri’u a lokacin zaɓe.
Shi kuwa Oyedepo, a ranar Lahadi ya bayyana cewa bai goyi bayan kowane ɗan takara ba. Sai dai bai fito ya ƙaryata tattauanawar da ya yi a waya shi da Peter Obi ba.
Discussion about this post