Wole Soyinka ya zargi Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele da laifin cin zarafi da ƙuntata wa ɗan Adam, wanda gagarimin laifi ne a duniya.
Ya ce Emefiele ya jefa rayuwar ‘yan Najeriya cikin ƙunci, talauci, wulaƙanci da tsananin wahala, sakamakon ƙarancin kuɗi a hannun ‘yan Najeriya da ya ƙaƙaba da sunan sauya launin kuɗi.
Soyinka ya yi wannan bayani a lokacin tattaunawar da Gidan Talabijin na Channels ya yi da shi.
Ya ɗora laifin kan Shugaba Muhammadu Buhari wanda shi ne ya ɗaure wa Emefiele gindi ya haifar da masifa a cikin ƙasa.
“Emefiele ya wulaƙanta ɗan Adam ta hanyar jefa shi cikin tozarta da ƙaƙa-ni-ka-yin yadda za su ciyar da kai da iyalai.
“Emefiele macuci ne, maƙetaci ne kuma mamugunci ne. Ubangiji ka tsare ni daga muguntar Emefiele.” Inji Soyinka.
“Wannan wace irin ƙeta da mugunta ce wannan? Sai da aka wayi gari na rasa ɗan canjin da zan iya sayen jarida. Guguru ma ya gagari mutum, da kuɗin sa a banki amma Emefiele ya tsiyata mutum. Ga mutum da amfanin noma a gona ya na so ya kawo kasuwa ya sayar, amma babu kuɗin motar da zai kai kayan kasuwa. Wannan wace irin ƙeta ce Emefiele ya gasa mana!”
Discussion about this post