Rundunar ‘yan sandan jihar Benue sun kama wasu matasa biyu da suka kashe wani tsoho Ihwakaa a kauyen Ikyve dake karamar hukumar Konshisha.
Ihwakaa ya gamu da ajalinsa bayan matasan kauyen sun zarge sa da tsafi.
Wani mazaunin kauyen da baya so a fadi sunnan sa ya ce rikicin ya somo ne bayan zaegin tsaya ya kashe dan Ihwakaa mai suna Henry, sirikarsa da jikarsa jaririyar a ranar daya.
Mazaunin ya ce ba tun yanzu ba mutanen kauyen na zargin tsohon da yin amfani da ruwa a ‘ kauyen domin yin tsafi da mutane.
“A dalilin haka ya sa matasa suka birne tsohon a rami da ransa domin a ganinsu wadannan mutane uku sun mutu ne saboda tsafin da tsohon ke yi.
Wani dattijo a kauyen mai suna Baba Agan ya ce duka dattawan kauyen za su zauna domin kada tarzomar ya wuce gona da iri.
“ Babu dadi abin da mutane suka yi na yin gaggawar daukan doka a hannun su ba tare da sun kira jami’an tsaro ba.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Catherine AAnene ta ce sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a aikata wannan mummunar abu.
Discussion about this post