Karin maganar da Hausawa ke cewa, ‘mai hali ba ya barin halin sa’, ta ƙara tabbata kan wani gawurtaccen mai laifin da ya arce daga Kurkukun Kuje tun a cikin Yuli 2022.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa ta samu sa’ar kama Salisu Buhari a cikin jihar, tare da wani abokin sa mai suna Zubairu Ali.
An kama su bayan sun saci babur a Ƙaramar Hukumar Nasarawa a Jihar Nassarawa.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel ne ya sanar da haka a ranar Lahadi, a Lafiya, babban birnin jihar.
“An damƙe gudajjen ne tare da wani abokin sa mai suna Zubairu Ali, bayan sun saci babur.
“Binciken farko-farko ya nuna cewa su biyun ke da alhakin satar kusan dukkan baburan da ake sacewa a Ƙaramar Hukumar Nasarawa da kewaye.
“Da aka tsananta yi masa tambayoyi, Salisu Buhari da kan sa ya shaida wa ‘yan sanda cewa daga Kurkukun Kuje ya arce lokacin da ‘yan ta’adda su ka kai wa kurkukun hari a cikin watan Yuli, 2022.
“Ya shaida wa ‘yan sanda cewa bayan ya gudu, sai ya haɗu da abokin sa, su ka shiga satar babura.”
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, Maiyaƙi Mohammed-Baba ya bada umarnin a maida binciken mai laifin zuwa Ofishin Binciken Masu Manyan Laifka da ke Lafiya.