Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi na farautar ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin APGA, Ifeanyi Odoh, bisa zargin hannu a kisan basarake Igbokwe Ewa.
A ranar waccan Litinin ce dai wasu da ba a san ko su wa ne ba su ka bindige basaraken a gidan sa.
Kafin mutuwar sa dai shi ne Basaraken Umu-Ezekoha a cikin Ƙaramar Hukumar Ezza ta Arewa.
Bayan kisan basaraken, sai APC ta yi zargin cewa Odoh ne da magoya bayan sa ke da hannu wajen kisan.
Sai dai kuma tuni Odoh ya ƙaryata zargin da APC ke yi masa. Ya ƙara da cewa a matsayin sa na wanda ya fito ƙaramar hukuma ɗaya da basaraken, tamkar uba ya ke a wurin sa.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi, Onome Onovwakpoyeya, ya fitar da sanarwa a ranar yau Litinin cewa ‘yan sanda na cigiyar ɗan takarar gwamnan na APGA da kuma wasu mutum tara.
‘Yan sanda sun ce duk wanda ya gan su, ko ya ji labarin inda wanin su ko su duka su ke, to ya sanar wa hukuma.
Idan ba a manta ba, a Kano ma ana tsare da Alasan Doguwa, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, bisa zargin kisa, banka wuta, riƙe bindiga da amfani da ita a wurin taro ba tare da lasisi ko izni ba.
Discussion about this post