A daidai ana kokarin karkare kamfen din neman kuri’u a wajen mutane kan zaben gwamna da ya tunkaro, a jihar Kaduna, Ɗan takarar gwamna na PDP, Isah Ashiru ya kara jaddada aniyarsa na ganin jama’ar jihar Kaduna sun ragargaji romon dimokuraɗiyya idan ya zama gwamnan jihar.
A jawabi da yayi da ke kama da rokon jama’ar jihar su zaɓe shi, Ashiru ya yi alkawarin rage kuɗin makaranta da ɗaliban jihar ke biya sannan kuma da bunƙasa harkokin noma a jihar.
Bayan haka kuma ya ce zai dawo wa jihar da martabar ta a idanun jama’a.
” Idan na zama gwamnan Kaduna, zan tabbatar da na bunkasa harkokin noma a faɗin jihar sannan kuma zan rage kuɗin makaranta da dalibai ke biya.
Sannan kuma ya ce duk wanda aka kora a jihar Kaduna zai dawo da su sannan waɗanda ba a biya su kuɗaɗen sallamarsu ba duk zai biya.
Isa Ashiru zai fafata da ɗan takarar gwamnan na AP, Sanata Uba Sani wanda ake yi wa ganin zai iya zama wa Ashiru ƙashin kifi a wuya a lokacin wannan zaɓe.